Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 201 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –53, Kaduna-74, Katsina-40, Rivers-11, Filato-9, Kwara-6, Bauchi-2, Ogun-2, Taraba-2, Edo-1 da Sokoto-1.
Yanzu mutum 73,374 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 66,314 sun warke, 1,197 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 5,888 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 25,005, FCT –8,424, Oyo – 3,760, Edo –2,738, Delta –1,829, Rivers 3,162, Kano –1,904, Ogun–2,330, Kaduna –3,941, Katsina -1,237, Ondo –1,751, Borno –758, Gombe –1,069, Bauchi –810, Ebonyi –1,061, Filato – 4,006, Enugu –1,363, Abia – 973, Imo –688, Jigawa –340, Kwara –1,232, Bayelsa –469, Nasarawa – 562, Osun –965, Sokoto – 193, Niger – 298, Akwa Ibom – 364, Benue – 501, Adamawa – 329, Anambra – 290, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 108, Ekiti –395, Taraba- 198, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.
Gwamnatin Najeriya ta ce a gaggauta sake bude cibiyoyin killace masu cutar korona, ganin yadda cutar ta sake darkakar kasar gadan-gadan ba sauki.
Ministan Harkokin Lafiya Osagie Ehanire ne ya bayyana haka a wurin taron Kwamitin Dakile Cutar Korona a ranar Alhamis, a Abuja.
Ya ce yin hakan ya zama wajibi, ganin yadda korona ta sake darkakar kasashen Turai gadan-gadan, tamkar wutar-daji.
Ya ce a wannan karo kowa na da rawar da zai taka wajen ganin wannan cuta ba ta sake fantsama ta yi wa al’ummar kasar nan mummunan illa ba.
“Mun ga yadda a ‘yan kwanakin nan ake ta samun karuwar masu kamuwa da cutar korona a kullum a kasar nan. Wannan kuwa ya sa mu tunanin sake barkewar cutar a karo na biyu.
“Dalili kenan na bada umarnin a gaggauta sake bude cibiyoyin killace masu cutar korona da cibiyoyin bayar da magunguna wadanda a baya aka rufe, saboda karancin masu dauke da cutar. Kuma a sake gaggauta kai jami’an lafiya a dukkan cibiyoyin.
Kasahen Turai na ci gaba da samun adadin masu kamuwa da cutar a kullum, fiye ma da yadda aka rika samu a baya.
Kasashe irin su Ingila, Portugal da Hungary tuni sun rigaya har sun kakaba dokar zaman gida tilas, ganin yadda adadin masu kamuwa a kullum har ma ya zarce yawan irin yadda ta rika kama mutane a watannin baya.
Abin ya kara muni da kamari a Amurka, inda a yanzu adadin wadanda su ka kamu a kasar ya haura mutum milyan 15.
Minista Ehanire ya shawarci ‘yan Najeriya su dauki kwararan matakan kare kai, musamman a lokacin Kirsimeti da sabuwar shekara, domin cutar korona ba hutu ta ke dauka ko jin fashin ranar da ba a iya kamuwa da ita ba.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya sha alwashin cewa na Najeriya na sane da irin yadda cutar ta sake barkewar sosai a Turai, kuma ana cikin shiri a kasar nan.
Ya ce duk wasu rigakafi ko maganin korona da za a sayar wa Najeriya, zai kasance sai Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ingancin su tukunna.
“Kuma ko an kawo su a nan kasar, sai likitocin mu da masu binciken magunguna sun auna sun tantance sahihanci tukunna.” Inji Mustapha.