Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya shiga ‘Kulle’ bayan wasu jam’an gwamnati da wasu daga cikin iyalansa sun kamu da Korona.
El-Rufai ya bayyana a shafinsa ta tiwita cewa zai killace kansa zuwa har a yi masa sabon gwajin cutar ranar Lahadi domin sanin matsayinsa.
Dalilin yin haka kuwa shine ganin yadda hatta wasu daga cikin iyalan sa da ke tare dashi sun kamu da cutar.
A Najeriya dai annobar ta sake barkewa tundaga makon jiya.
A jihar Kaduna mutum sama da 100 ne suka kamu da cutar ranar Juma’a baya ga daruruwan mutane da ka dauki jinin su suna jiran sakamakon gwaji.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 796 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum – 248, FCT-258, Kaduna-117, Katsina-52, Ogun-27, Kwara-23, Gombe-22, Adamawa-17, Filato-15, Kano-6, Rivers-2, Ondo-2, Ekiti-2, Nasarawa-2, Sokoto-2 da Taraba-1
Yanzu mutum 72,140 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 65,722 sun warke, 1,190 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 5,241 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 24,614, FCT –3,994, Oyo – 3,747, Edo –2,726, Delta –1,828, Rivers 3,116, Kano –1,880, Ogun–2,319, Kaduna –3,703, Katsina -1,171, Ondo –1,751, Borno –758, Gombe –1,069, Bauchi –802, Ebonyi –1,055, Filato – 3,994, Enugu –1,355, Abia – 926, Imo –681, Jigawa –340, Kwara –1,226, Bayelsa –466, Nasarawa – 541, Osun –965, Sokoto – 191, Niger – 298, Akwa Ibom – 362, Benue – 501, Adamawa – 304, Anambra – 290, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 108, Ekiti –391, Taraba- 196, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.