“Mutuwar jami’an kula da lafiyar mu a fagen famar yaki da cutar korona abin takaici ne matuka. Musamman saboda wadannan kwararrun likitoci su ne ke saida rayukan su domin kokarin ceton na mu rayukan.”
Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjina wa sadaukar da rayukan da likitoci 20 su ka yi, wadanda su ka rasa rayukan su a aikin agajin ceton masu fama da cutar korona a cikin mako daya.
Wannan jimami da ta’aziyya ta Buhari na cikin bayanan da wasikar da ya aika wa Kungiyar Likitoci ta Najeriya, wadda ta bada sanarwar mutuwar likitoci 20 masu aikin ceton rayukan masu fama da cutar korona, a jihohi daban-daban na kasar nan.
Da ya ke nuna alhinin rashin su, Shugaba Buhari ya bayyana cewa, “Mutuwar jami’an kula da lafiyar mu a fagen famar yaki da cutar korona abin takaici ne matuka. Musamman saboda wadannan kwararrun likitoci su ne ke saida rayukan su domin kokarin ceton na mu rayukan.”
Ya kara da cewa, “jami’an kula da lafiyar mu na sadaukar da na su rayukan a fadin kasar nan domin ceton rayuka. Saboda haka wannan gwamnatin ba za ta gajiya ba har sai ta tabbatar da cewa ta biya wa wadannan jami’an kula da lafiya dukkan bukatun su.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa, yayin da cutar korona ta dawo gadan-gadan, Shugaban Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA), ya bayyana cewa likitoci 20 su ka mutu a wannan makon sanadiyyar cututtuka masu alaka da korona.
Enema Amodu ya bayyana wannan tashin hankali a ranar Juma’a wurin taron manema labarai, inda ya ce wadanda su ka mutu din sun hada da jami’an lafiya da na tuntuba da wasu farfesoshi da tantagaryar likitoci.
Ya ce yawan wadanda ke mutuwar na karuwa a kullum.
“Mu da ke aikin harkokin kula da lafiya, mun rasa abokan aikin mu da dama. Wadanda korona ta kashe a cikin mako daya kadai a fadin kasar nan, sun kai likitoci 20.” Inji shi.
Jami’an kiwon llafiya na fadawa tarkon saurin kamuwa da cutar, saboda su ne ke fara tunkarar wanda ya kamu da cutar.
Duk da cewa su kan su jami’an kula da lafiya da likitocin su kan su ana gargadin su rika amfani da rigunan kariya daga hada jiki da wanda ya kamu da korona, da yawan su ba su da sukunin samun kayan kariyar.
Idan ba a manta ba, sama da jami’an kula da lafiya 1,000 ne su ka kamu da cutar korona a Najeriya.
Hukumar Kula da Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (WHO), ta ce zuwa Yulin da ya gabata sama da jami’an kula da lafiya 10,000 ne suka kamu da cutar korona a fadin Afrika.
Sai dai zuwa yanzu ba za a ma iya tantance adadin yawan jami;an kiwon lafiyar da su ka kamu ba a Najeriya.
Amodu ya yi gargadin a tashi tsaye wajen kare kai daga kamuwa, domin a yanzu da korona ta sake dawowa, ta fi ta baya karfi da saurin kassara mutane gadan-gadan.
Ya ce a yanzu jama’a ba su daukar matakan kariya da muhimmanci, kuma babu kayan kariyar a wurare da dama, kamr yadda aka rika sayarwa a watannin baya, farkon bullar cutar.