Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 838 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –253, FCT-297, Filato-82, Kaduna-57, Katsina-32, Nasarawa-31, Kano-25, Gombe-24, Oyo-8, Rivers-8, Zamfara-7, Ogun-4, Bauchi-4, Edo-4, Anambra-1 da Sokoto-1.
Yanzu mutum 84,414 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 71,034 sun warke, 1,254 sun rasu.Sannan kuma zuwa yanzu mutum 12,126 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Juma’a, mutum 829 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Kaduna, Rivers, Kano da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 28,741, FCT –11,354, Oyo – 3,893, Edo –2,830, Delta –1,868, Rivers 3,376, Kano –2,194, Ogun–2,455, Kaduna –4,940, Katsina -1,602, Ondo –1,798, Borno –796, Gombe –1,272, Bauchi –964, Ebonyi –1,097, Filato – 4,541, Enugu –1,382, Abia – 983, Imo –748, Jigawa –392, Kwara –1,379, Bayelsa –519, Nasarawa –721, Osun –1004, Sokoto –298, Niger – 409, Akwa Ibom – 429, Benue – 532, Adamawa – 355, Anambra – 308, Kebbi – 163, Zamfara –86, Yobe – 187, Ekiti –409, Taraba- 211, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.
Sake barkewar cutar korona gadan-gadan a kasar nan ta haifar da sanarwa cewa kada daliban jami’a su yi gaggawar komawa makarantu. Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ce ta fitar da wannan sanarwa.
NUC ta ce duk da a yanzu an cimma matsayar sasantawa tsakanin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa da kuma Gwamnatin Tarayya, to dalibai su ci gaba da zama a gida, babu batun gaggawar sake bude jami’o’i bayan Kirsimeti da bukukuwan sabuwar shekara.
Wannan sanarwa da NUC ta fitar, ta zo ne ganin yadda korona ta sake barkewa fiye da yadda ta fantsama a farkon bullar ta.
Cikin makon da ya gabata dai an samu wadanda su ka kamu da cutar korona fiye da mutum 5000 a Najeriya, adadin da ba ta taba samun yawan haka a cikin mako daya a kasar nan ba.
NUC ta kuma umarci Shugabannin Jami’o’i kada su bari ana gudanar da wasu tarurruka a cikin jami’o’in wadanda dandazon jama’a za su yi cincirindo a wurin.
Sanarwar da Mataimakin Shugaban NUC a fannin Tsarin Mulki, Chris Maiyaki ya sa wa hannu, ya umarci shugabannin jami’o’i cewa dukkan dakunan kwanan dalibai, ajujuwan karatu da dakunan taro su ci gaba da kasancewa a kulle.