Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 617 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –225, FCT-181,Kaduna-125, Adamawa-25, Nasarawa-20, Kano-12, Rivers-8, Edo-4, Ekiti-4, Bayelsa-3, Ogun-3, Filato-3, Akwa Ibom-2, Delta-1 da Sokoto-1.
Yanzu mutum 72,757 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 65,850 sun warke, 1,194 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 5,713 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 24,839, FCT –8,338, Oyo – 3,747, Edo –2,726, Delta –1,829, Rivers 3,124, Kano –1,892, Ogun–2,322, Kaduna –3,828, Katsina -1,171, Ondo –1,751, Borno –758, Gombe –1,069, Bauchi –802, Ebonyi –1,055, Filato – 3,997, Enugu –1,355, Abia – 926, Imo –681, Jigawa –340, Kwara –1,226, Bayelsa –469, Nasarawa – 561, Osun –965, Sokoto – 192, Niger – 298, Akwa Ibom – 364, Benue – 501, Adamawa – 329, Anambra – 290, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 108, Ekiti –395, Taraba- 196, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.
Masana ilmin hada magunguna dake aikin hada maganin rigakafin cutar Korona sun ce nan da karshen 2021 kowa da kowa zai samu maganin rigakafin cutar Korona.
Malaman dake aiki da kamfanin BioNTech da Oxford ne suka fadi haka a taron tattauna hanyoyin dakile yaduwar cutar da UN ta shirya.
Zuwa yanzu kasar UK ita ce ƙasa ta farko a duniya da ta amince da maganin rigakafin korona da kamfanonin Pfizer da BioNTech suka hada.
Gwajin sahihanci da ingancin maganin da hukumar MHRA ta yi ya kai kashi 95.
Tuni wadannan kamfanonin sun fara yi wa mutane allurar rigakafin cutar da maganin da suka hada a Disamba.
Discussion about this post