KIWO KORE TALAUCI: An fara koya wa matasa 17,000 yadda ake samun kuɗi da kiwon zomaye

0

Shugaban Hukumar Bunkasa Dabarun Noma ta Kasa (NALDA), Paul Ikanne, ya bayyana cewa za a koya wa matasa musamman na kudancin kasar nan dabarun kiwon zomaye.

Ikanne wanda ya ke magana da manema labarai a Abuja, ya ce matasa 17,000 ne za su ci gajiyar wannan shiri, kuma tuni har an fara a wasu jihohin na kudancin Najeriya.

“Wannan shiri zai kasance ana farawa ne rukuni-rukuni. Kuma tuni rukunin jihohin farko da su ka hada da Imo, Abia, Cross River da Oyo har matasan da za su ci gajiyar shirin sun samu horo tare sa kyautar tallafin zomayen da za su fara kiwo.

“Idan kun tuna Shugaba Muhammadu Buhari ya bullo da shirin tallafa wa matasa harkokin kasuwancin noma. A karkashin shirin matasa daga kananan hukumomin kasar nan 774 za su amfana. To tuni har an kaddamar an fara a wasu jihohin, inda aka fara aikin bunkasa harkokin noman samun kudi a zahirance a zukatan matasa, ta hanyar farawa da kiwon zomaye.

“Shugaba Buhari ya amince kuma ya tanadar wa wannan hukuma da kudaden gudanar da wannan gagarimin shirin ba tare da jikara ko tunanin samun tangarda ba.” Inji shugaban na NALDA.

“Jama’a da dama ba su san albarka da alherin da ke tattare da harkokin kiwon zomaye ba.

“Kiwon zomo sana’a ce mai kawo kudi, saboda zomo ya na da daraja. Ba za ka taba kiwata zomo ba tare da ka ci riba ba.

“Naman zomo kudi ne, fatar zomo kudi ce. Kashin zomo kai har da fitsarin sa idan ka sayar, kudi za ka samu a tsanake.” Inji Ikanne.

Daga nan ya ce hukuma ce da kan ta za ta rika sayen fatar zomayen da kashi da fitsarin su daga wurin matasan da za su rika yin sana’ar kiwon zomayen.

“Kowane matashi akalla zai rika samun cinikin naira 100,000 kowane wata daga sayar da zomaye, kashin su, fitsarin su da kuma fatun su.”

Ya kara da cewa yanzu a duniya naman zomo na sahun gaba na naman da ake rububi, saboda dadin sa, ga shi fari kuma shi likitoci su ka shawarci masu taiba su rika ci, domin su rage kitse a jikin su.

“Sannan kuma masu yin takalman zamani masu tsayar tsiya na kwalisa, wato ‘designer shoes’, sun fi bukatar fatar zomo, ta fi daraja, sun fi sayen ta da tsada.”

Share.

game da Author