KISAN MIJI: Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kisan Maryam Sanda

0

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke wa Maryam Sanda kan kisan mijinta, Biliyaminu Bello.

Kwamiti mai mambobi uku na kotun daukaka kara karkashin jagorancin Justis Stephen Adah, a ranar Juma’a, ya yi watsi da daukaka karar na Maryam Sanda.

Kotun ta ce dalilai 20 na daukaka kara da ta gabatar a gaban kotun ba su gamsar da ita don haka aka yi watsi da su.

Babbar Kotun Tarayya karkashin jagorancin Mai Shari’a Yusuf Halilu a Babban Birnin Tarayya ta yanke wa Maryam Sanda hukunci kisa kan kisan mijinta a gidansu da ke Abuja da tayi a shekarar 2017.

Alkalin kotun ya ce an gano cewa iyaye da ƴan uwan Maryam sun nemi boye duka shaidun da zasu nuna lallai itace ta kashe mijin ta, wanda hakan ya sake nutsar da su cikin tabbatar da rashin gaskiyarsu a gaban kotu.

Yanzu dai dama daya ya rage wa Maryam Sanda, shine ta garzaya Kotun Koli.

Share.

game da Author