KISAN GILLAR ZABARMARI: Muddun mutane suka cigaba da tona mana asiri, za mu cigaba da Kashe su – Boko Haram

0

Kungiyar Boko Haram ta ikirarin cewa muddun mutane suka cigaba da tona musu asiri suna kama ƴan kungiyar suna mika wa jami’an tsaro su ma ba za su daina yi wa mutane kisan gilla ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga yadda Boko Haram suka yi wa wasu manoma 43 kisan gilla a daidai suna aikin girbin shinkafa a gonar su.

Sai da maharan suka yi musu zobe a gona sannan suka rika yi musu yankan rago.

A bidiyon mai magana wanda ya rufe fuskarsa da kyalle ya yi kira ga mutane da su tuba.

” Idan kuka tuba za mu kyale ku, idan kuka ki za mu karkashe ku. Wannan shine sakon mu zuwa ga mutane baki daya.

Har yanzu dai ƴan Najeriya na jimamin kisan gillar da mahara suka yi wa manoma 43 a garin Zabarmari jihar Barno.

Share.

game da Author