KISAN GILLAR ZABARMARI: Majalisar Tarayya ta aika wa Buhari Sammaci, ya gaggauta bayyana a gabanta

0

Majalisar tarayya ta aika wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari da sammaci ya gaggauta bayyana a gabanta.

Gaba daya ‘yan majalisan sun amince Buhari ya gaggauta bayyana a gaban majalisar domin ya amsa tambayoyi musamman game da tsaro da kisan gillar da ak yi wa manoma a Zabarmari.

Dan majalisa Satomi Ahmed ya mika wata kudirin gaggawa a gaban ‘yan majalisar kan kisan gillar da aka yi wa wasu manoman shinkafa 40 a garin Zabarmari, jihar Barno.

Yadda Boko Haram suka kashe manoman shunkafa 44 a jihar Barno

Akalla manoman shinkafa sama da 40 wasu mahara da ake zaton Boko Haram ne suka yi wa kisan gilla a tsakiyar gonakinsu a daidai suna aikin girbi.

Dan majalisar Tarayya dake wakiltar yankin Ahmed Satomi, da aka kai wa hari ya shaida haka yana mai cewa zuwa yanzu an mika musu gawarwakin manoma 44 da aka yi wa kisan gilla a gonakin su, wanda za a rufe ranar Lahadi.

” Manoma da masu kamun kifi 44 da aka kawo mana gawarsu zuwa yanzu. Duka wadannan manoma na aiki ne a wani katafaren gonan shinkafa da ke garin Garin-Kwashebe.

An yi jana’izan mamatan ranar Lahadi a Zabarmari.

Shawarar gwamna Babagana Zulum ga Buhari

Gwamnan jihar Barno ya shawarci tawagar gwamnatin tarayya da suka kawo masa jaje, da yi masa ta’aziyyar kisan gillan da Boko Haram suka yi wa manoma sama da 40 a kauyen Zabarmari.

Tawagar gwamnatin Tarayya ya isa garin Maiduguri ranar Litini sannan sun gana da gwamnan jihar Babagana Zulum.

Daga nan sai suka dunguma zuwa garin Zabarmari domin yi wa mutane da iyalan mamatan ta’aziyya.

A jawabinsa Zulum ya shawarci gwamnatin tarayya ta yo hayan zaratan sojoji daga kasashen waje su zo su gama da Boko Haram tunda abin yaki ci yaƙi cinyewa.

Daga nan sai ya ba gwamnati shawara kamar haka:

1 – Ga dubban matasa nan da basu da abin yi, me zai hana Gwamnati daukan su aikin soja da ɗan sanda ba domin kara yawan jami’an tsaro a kasar nan.

2 – Gwamnati ta nemi hadin kai da taimakon gwamnatocin kasashen dake makwabtaka da Najeriya domin kakkabe sauran maboyan Boko Haram dake kan iyakokin kasashen.

3 – Sannan kuma ina kira ga gwamnati ta dauko hayan sojoji daga waje su shigo su kakkabe sauran maboyan Boko Haram dake Sambisa, su share mana ita tas.

4 – Gwamnati ta samar wa jami’an tsaro da manyan motocin yaki da kuma makamai masu masu nisan zango na zamani.

5 – Muna kira ga gwamnatin tarayya ta agaza wa jihar domin dawo da ƴan asalin ƙasar har dake zaman gudun hijira a kasashen Kamaru, Nijar da Chad, su dawo gida hakanan.

6 – Ina rokon gwamnatin tarayya ta kawo ayyukan cigaba a jihar Barno, cewa gwamnati ta yi watsi da jihar babu wani aikin cigaba da take yi a kasar har.

Ya ce rashin ababen more rayuwa ma na daga cikin abubuwan da ke ci wa gwamnati tuwo a kwarya a jihar.

” Baya ga shekara 11 da jihar ke fama da hare-haren Boko Haram, yanzu kusan shekara 25 kenan rabon da ace wai gwamnatin tarayya ta kawo wani aikin cigaba, cikin jihar Barno, da wasu jihohin Arewa maso Gabas.

” Idan da gwamnatin tarayya za ta iya gyara titunan jihar da za a samu sauki matuka.

A nashi jawabin, jagoran tawagar gwamnatin tarayya, Shugaban majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya ce Buhari ya nuna rashin jin dadin sa ga kisan gillan da aka yi wa wadannan manoma.

Sannan kuma ya ce gwamnati za ta ci gaba da aiki tukuru wajen ganin an kawo karshen wannan ta’addanci na Boko Haram da rashin tsaro da ya addabi ƴan Najeriya.

Tawagar gwamnatin tarayyar ya hada da shugaban gaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno da wasu manyan jami’an gwamnati.

Share.

game da Author