Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta janye rahoton da ta bayar da farko cewa mutum 110 ne aka kashe a harin yankan ragon da Boko Haram su ka kai wa manoma a kauyen Zabarmari.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa mutum 43 ne aka kashe, kamar yadda a ranar Lahadi, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno ya shaida wa manema labarai cewa mutum 43 ne aka yi wa yankan rago.
A yammacin Lahadin ce kuma Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Edward Kallon ya fitar da sanarwa cewa wadanda Boko Haram su ka kashe a Zabarmari za su kai mutum 110 a Gonar Shinkafa ta Koshobe.
Amma daga baya a ranar Litinin, jami’in yada labarai na UN a Najeriya ya ce takardar bayanin adadin da ya fitar a madadin Kallon, ba hakikanin gaskiyar adadin ba ne, kamar yadda UN ta sake tabbatarwa daga baya.
A wani e-mel da jami’ar mai suna Sabbagh ta tut-tura wa gidajen jaridu, ta ce manema labarai su yi watsi da wancan ikirarin kisan mutum 110.
“Don Allah ina so ku yi watsi da waccan sanarwar farko da muka ce mutum 110 ne aka yi wa yankan rago. Domin ba mu tabbatar da sahihancin adadin ba.”
A yanzu hukumar kula da masu gudun hijirar ta majalisar Dinkin Duniya, ta maye gurbin adadin “mutum 110” da “adadin da ba a tabbatar da yawan su ba.”
Hukumar ta kara da cewa amma wasu da dama sun ji ciwo, baya ga wadanda aka kashe. ”
Wasu mazauna kauyen Zabarmari sun shaida wa wakilin PREMIUM TIMES a lokacin da ya isa kauyen cewa masu ceton gawarwaki sun bazama cikin daji domin laluben ko da akwai wasu gawarwakin a cikin dazukan.
“Adadin wadanda aka kashe din dai har yau daga mutum 43 ba mu sake tsintar ko da wata gawa daya ba. Amma dai mun san cewa ma’aikatan da ke cikin gonar sun kai mutum 70.” Inji majiyar.