KIRSIMETI: Buhari ya nemi ‘yan Najeriya su amince cewa gwamnatin sa za ta iya magance rashin tsaro

0

“Har a zuciya ta na dauki cewa tabbatar da tsaro a kowane dan Najeriya kamar wani shika-shikan imani ne.” Inji Buhari.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake rokon ’yan Najeriya su kara juriyar amincewa da mika wuya ga gwamnatin sa, su yarda cewa zai iya magance matsalar tsaro a kasar nan.

Haka ya jaddada a sakon murnar bukukuwan Kirsimeti da ya aika wa ’yan Najeriya a ranar Alhamis.

A sakon wanda aka aiko a ofishin PREMIUM TIMES, Buhari ya ce, “Ni ina ji cikin zuciya ta cewa tabbatar da tsaron rayukan ‘yan Najeriya wani shika-shikan imani ne a wuri na. Samar da tsaron nan na daga daga cikin ajandodin wannan gwamnatin run daga farkon kafa ta.” Cewar Buhari.

Kusan ko’ina a cikin yankunan kasar nan na fama da matsalar rashin tsaro. A watan Nuwamba an kashe mutum sama da 300, sannan aka yi garkuwa da mutum 290.

Haka nan kuma a cikin wata sanarwar, buhari ya yi umarnin cewa saboda barkewar cutar korona, ba za a je masa gaisuwar murnar ranar Kirsimeti ba.

Cikin sakon san a murnar Kirsimeti, Buhari y ace, “Ina taya Kiristocin kasar nan ‘yan uwa na maza da mata murnar tare da dukkan sauran ‘yan Najeriya saboda ranar farin ciki, ranar haihuwa AnnaBI Isa (AS).

“ A addinin Kirista, lokutan shagulgulan Kirsimeti na matsayin rnakun farin ciki, zaman lafiya, fata nagari, so da kaunar juna, da kuma neman tsira. Wadannan halaye da dabi’u nagari ne Annabi Isa (AS) ya koyar, kuma a yanzu irin su ne mu ke bukata kasar nan ta ginu a kan su, daidai lokacin da mu ke fuskantar kalubale daga bangarori daban-daban. Ga masu garkuwa, ga Boko Haram, ga matsin tattalin arziki da kuma sake barkewar cutar korona.

Buhari ya kara jaddada kudirin gwamnatin sa na kara karfafa tsaro da karfafa sojojin Najeriya da sauran bangarorin jami’an tsaro domin magance matsalar tsaro.

Ya umarci jami’an tsaro su kara kaimi, kuma ya gode kan kokarin da sub ke yi. Ya nemi su rubanya kamar yadda su ka tashi tsaye haikan su ka ceto daliban Kangara 344 da aka ci garkuwa da su a jihar Katsina, makonni biyu da suke wuce.

“Ni ina ji cikin zuciya ta cewa tabbatar da tsaron rayukan ‘yan Najeriya wani shika-shikan imani ne a wuri na. Samar da tsaron nan na daga daga cikin ajandodin wannan gwamnatin run daga farkon kafa ta.” Cewar Buhari.

Share.

game da Author