KASAFIN 2021: Ko Shugabannin Hukumomi su tara haraji da yawa ko na tara masu gajiya – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa Kasafin 2021 na naira tiriliyan 13.588 hannu a ranar Alhamis, inda a lokacin da ya ke sa hannun, ya gargadi hukumomin tara kudaden haraji daban-daban cewa su tabbatar sun tara kudaden haraji kan lokaci. Ko kuma ya tara masu gajiya.

Yayin da Buhari ya sa wa kasafin na 2021 hannu ya zama doka, ya ja kunne cewa, “mu na kara zafafa kokarin tara kudaden harajin cikin gida ne, domin mu samu isassun kudaden da za mu iya gudanar da ayyukan da ke cikin kasafin da su.

“Saboda haka dukkan hukumomin tara kudaden harajin cikin gida da Ma’aikatu da Hukumomi da Cibiyoyi da Kamfanoni ko Masana’antu na gwamnati, tilas fa su tashi tsaye su tara adadin harajin da mu ke bukata. Su tabbatar sun rage hanyoyi na kashe kudade barkatai. Kuma su tabbatar cewa duk abin da su ka karba a matsayin haraji, to su na damka wa asusun ajiyar gwamnatin tarayya, ba tare da ko sisin kwabo ya salwanta ba.”

Kasafin dai wanda Buhari ya sa wa hannu, na naira tiriliyan 13.588 ne. Kuma yanzu ya zama doka, bayan sa masa hannu da ya yi a ranar Alhamis din, wato ranar jajibirin sabuwar shekara ta 2021.

“Hukumomin da harkokin mai su ka rataya a wuyan su, su tabbatar cewa an samu nasarar da ake so a cimma a bangaren danyen man fetur. Shugabannin Hukumomin da su ka kasa tara adadin harajin da ya kamata su tara a kan lokaci, to za su ji a jikin su.

“Sannan kuma ina ina kara kira ga daukacin ‘yan Najeriya da manyan ‘yan kasuwa kowa ya sauke nauyin da ke wuyan san a biyan haraji a kan kari.” Inji Buhari.

Shi dai wannan kasafi na naira tiriliyan 13.588, fiye da naira tiriliyan 4 da za a kashe duk babu ita, babu dalilin ta, sai an ciwo ba tukunna.

Share.

game da Author