KANKARA333: Mu muka sace daliban sakandare a Katsina – Boko Haram

0

Boko Haram sun dauki nauyin yin garkuwa da daliban sakandare na Makarantar Kimiyya ta garin Kankara a jihar Katsina.

Yayin da wasu su ka tsere a lokacin, an tabbatar da sace dalibai 333 a ranar Juma’a da dare da aka kai harin.

Har yanzu dai gwamnatin Najeriya ba su yi wata magana batun bayan da Boko Haram su ka yi ikirarin kama yaran.

Masanin harkokin tsaro Kabir Adamu ya ce ya na ganin ‘yan bindiga ne dai su ka kama yaran amma ba Boko Haram ba.

“A yanzu dai za mu iya cewa masu garkuwa ne suka kama yaran, ba Boko Haram ba. Amma fa kowa ya san Boko Haram sun kutsa yankin, har ma sun kulla yarjejeniya tsakanin su da ‘yan bindiga, wadanda su ka ce su hade da juna, har ma su bai wa ‘yan bindigar horo.” Inji Adamu.

“Sannan kuma akwai wasu bidiyo da ake watsawa a can baya, inda masu garkuwa na nan Arewa maso Yamma ke bayyana yi wa Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau biyayya.” Inji Adamu.

Shekaru biyar bayan Buhari ya yi alkawarin kakkabe Boko Haram, har yanzu dai sai tuma tsalle wuri daya ake yi an kasa gudu.

Tuni dai jihohin Katsina, Kano da Jigawa sun bayyana gaggauta rufe makarantun su.

Masu lura da lamarin kasar nan na tsoron cewa kada a tilasta wa yaran daukar makami su ma su shiga cikin mahara.

Kabiru Adamu mai Becon Security Group, ya ce “Abin da ya faru a Kankara jihar Katsina, ya taba faruwa a Zamfara, Kaduna, Lagos, Ogun da Yobe, inda aka arce da dalibai, kuma babu wani da aka hukunta.”

Kan haka ya ce “in dai batun shari’a a kasar nan ce, to a lalace ta ke kawai.”

Daruruwan jama’a ne su ka hau kan titi a Katsina su ka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari zanga-zangar haushin sakacin da gwamnatin sa ta yi har ‘yan bindiga su ka sace dalibai 33 a sakandaren kimiyya ta Kankara.

Washegarin sace yaran jami’an tsaron Najeriya sun ce sun yi batakashi da maharani, amma ba su ce ga yadda ta karke ba.

An sace daliban a ranar Juma’a 11 Ga Disamba, sa’o’i biyar bayan saukar Buhari gida a Daura domin zuwa yin hutun mako daya.

Washegari Asabar Gwamna Aminu Masari ya je Kankara a makarantar, inda ya shaida wa dubban iyayen yara cewa su kwantar da hankullan su, za a ceto yaran cikin ruwan-sanyi.

Bayan kwana biyu Masari ya bayyana cewa an tantance tare da tabbatar da cewa an gudu da dalibi 333.

A ranar Litinin kuma Ministan Tsaro Bashir Magashi, ya je Katsina, inda ya shaida wa gwamnan cewa za a ceto yaran cikin kankanin lokaci, domin an ga inda aka boye su.

Bayan Masari ya kai wa Buhari rahoton halin da ake ciki dangane da satar yaran, inda ya same shi a Daura, ya ce Gwamnatin Tarayya na magana baki-da-baki da masu garkuwar, kuma ceto to cikin ruwan sanyi.

Su kuma ‘yan Najeriya na ci gaba da nuna fushin yadda Buhari ya ki kai ziyarar jaje a Kankara, duk kuwa da cewa jihar sa ce, kuma shi na cikin jihar aka yi garkuwar da daliban.

Dangane da sace daliban, mazauna Kankara sun nuna fushin su, kamar yadda wani mai suna Salihu Bamle ya ce hankalin su ya tashi matuka.

“Yan bindigar nan sun iso garin mu Juma’a da dare, sai da su ka fara shiga cikin gari, su ka rika harbin firgita jama’a, sannan su ka zarce makarantar, su ka yi gaba da dalibai masu yawa.”

Masari ya kulle makarantar, washegarin Asabar lokacin da ya kai ziyara. Ya kulle har da dukkan sauran makarantun jihar baki daya.

Wannan ne mummunan harin garkuwa da dalibai, tun bayan Harrin da Boko Haram su ka kai a Chibok, Jihar Barno, inda su ka yi garkuwa da dalibai mata 276.

Har yanzu akwai dalibai mata 112 a hannun Boko Haram sauran matan Chibok, tun cikin 2014.

Masu lura da lamarin kasar nan na tsoron cewa kada a tilasta wa yaran daukar makami su ma su shiga cikin mahara.

Kabiru Adamu mai Becon Security Group, ya ce “Abin da ya faru a Kankara jihar Katsina, ya taba faruwa a Zamfara, Kaduna, Lagos, Ogun da Yobe, inda aka arce da dalibai, kuma babu wani da aka hukunta.”

Kan haka ya ce “in dai batun shari’a a kasar nan ce, to a lalace ta ke kawai.”

Share.

game da Author