KANKARA 333: Yadda makiyaya su ka ceto min yaro na – Aminu Male

0

Wani mutum mai suna Aminu Male, ya bayyana yadda wasu makiyaya su ka cinto dan sa a jeji, bayan ya kubuta daga hannun wadanda su ka saci daliban sakandare su 333 a Kankara, Jihar Katsina.

Male ya ce makiyayan ne su ka tsinto dan sa, kuma su ka kai shi masa dan gida.

Tuni dai Boko Haram su ka yi ikirarin sace yaran, kamar yadda wani faifai ya bayyana Shekau na bayani.

Yaron mai suna Usama, ya na da shekaru 17, sannan ya na babban aji na SS2 a Sakandaren Kimiyya ta Kankara.

Bayan an kai masu hari an tafi da su a ranar Juma’a tsakar dare, ya taki sa’ar kubuta, aka maida shi gida ranar Lahadi.

Dalibin ya shaida wa baban sa cewa an rika yi doguwar tafiya da su a cikin surkukin jeji mai nisan gaske.

Ya ce sai cikin dare ne kawai ake tarkata su a tasa su gaba ana kara nausawa cikin jeji da su. Ya ce amma da rana ana boye su cikin bishiyoyi masu duhu, don kada jiragen helikwafta masu shawagi su gano su.

Daga Bakin Usama: Yadda Na Kubuta:

“Ranar Asabar mu na zaune a wani wuri da aka boye mu, mun fara shirin nausawa gaba kenan, na ji mahara sun a cewa nan gaba akwai wani gari. Kuma ta tunanin shin a kutsa da mu ta cikin garin ko kuwa a kewaye kada a shiga ta ciki?

“Su na ta wannan gardamar, ni kuma ina ta addu’a, can sai na mirgina bayan bishiya, har aka yi gaba aka bar ni a wurin. Dama kuma kafa ta daya ta samu rauni, tafiyar ma da kyar na ke yi.

“Bayan wani tsawon lokaci sai na kasara wani kauye, wanda na ji mahara din na magana.” Haka baban yaron ya ce dan na sa ya shaida masa.

Ya ce dan nasa ya isa kauyen cikin dare, ya samu wani masallaci ya shige.

“Na kama kofar masallacin na bude, na kwanta, na kama barci. To tarin da na rika yi ne har wani mutum ya ji ni, wanda shi ma a cikin masallacin ya ke kwance ya na barci.

Ya ce mutumin ya ji tausayin sa, ya yi alkawarin zai taimake shi.

“Da safiya ta yi, sai su ka ba shi wando, domin ya sa a kan kayan sa na makaranta, don kada a gane dalibin da aka sato ne. A haka ya saje da mutanen yankin.

“ Mutumin da ya taimake shi din ne ya sanar da wasu Fulani da ke wajen, su kuma su ka shirya da mai babur, ya dauke shi ya kai shi har cikin Kankara.

“To shi kuma mai babur ya kai shi unguwar Zango. Daga can kuma ya samu wani mai babur din ya kawo shi har gida.” Haka mahaifin yaron ya bayyana.

“Yaron ya shaida min ba a ba su abinci ba, sai dai su ka rika cin ganyen itatuwa da ruwan tabki.” Inji mahaifin yaron.

Share.

game da Author