Kamfanin Sufurin Jiragen Arik Air ya sallami ma’aikata 300

0

Kamfanin Sufurin Jiragen Arik Air ya sallami ma’aikata 300. An sanar da wannan sallamar a ranar Juma’a.

Wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Arik Air, Adebanji Ola ya fitar, ya ce sallamar ma’aikatan 300 ta zama wajibi, sakamakon yadda barkewar korona ta durkusar da harkokin sufurin jiragen sama.

Sanarwar ta ce wadanda aka sallama din dukkan su zaman-kashe-wando kadai su ke yi a kamfanin, babu wani takamaimen aikin da su ke yi, saboda harkoki ba su tafiya daidai.

Sai dai kuma Arik Air ya ce duk da an sallame su, za a bi kowanen su a ba shi ‘yan kudaden taya su zaman hakuri a gida.

“Matsalar barkewar korona da matsin tattalin arzikin da korona ta haddasa, rashin samun riba a zirga-zirgar jirage da wasu matsaloli sun tilasta wa Arik Air sallamar ma’aikata 300.”

Arik Air ya ce ko ma an bar su ba a sallame su ba, to babu wani aikin da za su yi a kamfanin, domin zaman dirshan kawai su ke yi.

Sanarwar ta kara da cewa dama kuma sama da kashi 50 cikin 100 na ma’aikatan Arik Air, duk ba albashi su ke karba ba tsawon watanni shida, sai dai a dan damka masu dan alawus.

Arik Air ya yi wa ma’aikata 300 da ya sallama fatan alheri.

Share.

game da Author