Jirgin sama ya yi luguden wuta kan ƴan bindiga a surkukin dajin Kaduna -Hedikwatar Tsaro

0

Hedikwatar Tsaro ta bayyana cewa an kashe ‘yan bindiga masu yawan gaske, a wani harin bazata da sojojin sama su ka kai wa wani sansanin su a Dajin Kudaru, cikin Jihar Kaduna.

Kakakin Hedikwatar Tsaro John Enenche ne ya bayyana haka a ranar Lahadi a Abuja, inda ya ce an yi wa ‘yan bindigar raga-raga ne a ranar Asabar.

Manjo Janar Enenche, ya ce an samu rahotannin sirrin inda maharan su ka yi sansani ne, bayan sun kai wa sojoji hari.

“Daga nan sai aka tashi Sojojin Sama daga Rundunar Operation Thunder Strike, su ka dauki jirkin yakin sojojin Najeriya, su ka yi wa sansanin ‘yan bindigar luguden wuta, su ka kashe da dama.

Enenche ya ce zaratan ‘yan sanda kuma sun kai daukin farmaki daga kasa, inda su ka yi wa maharan kofar-raggo, suna kai hari daga hanyar Sarkin Pawa har Tawali zuwa Kofa.

Idan ba a manta ba, cikin makon jiya Rundunar Sojojin Najeriya ta bada sanarwar kashe ‘yan bindiga sama da 80 a dazukan Kaduna da Katsina da Katsina da Zamfara.

Share.

game da Author