Jerin kamfanoni 34 da Gwamnatin Buhari ta dauke wa biyan haraji

0

Kamfanin Lafarge, Jabi Mall da Grand Pela ne uku daga cikin kamfanonin da Najeriya ta dauke wa biyan haraji a kasar nan.

Wani rahoto da Hukumar Bunkasa Hannayen Jarin Kamfanoni ta Najeriya ta buga ne ya tabbatar da wannan rahoto.

Gwamnatin Tarayya na yafe wa wasu kamfanoni da masana’antun da ke taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.

Ana yin la’akari ne da kuma irin muhimmancin su wajen jayo masu hannayen jari domin kawo bunkasar ci gaban kasa.

Ana dibar kamar shekaru uku ba tare da sun biya harajin ko sisi ba daga tashin farko. Sai dai kuma ana sake daga masu kafa tsawon shekaru biyu ko daya kawai.

Hukumar NIPC ke da alhakin dauke masu harajin, ta hannun Ma’aikatar Cnikayya da Masana’antu ta Tarayya.

Jimlar yawan ma’aikatan da ke karkashin wadannan kamfanoni sun kai mutum 6,550. Wannan adadi kuwa idan aka duba, su na taimakawa wajen samar wa matasa aikin yi da kuma rage zaman-kashe-wando.

Wasu daga cikin kamfanonin masana’antun sarrafa kaya daban-daban su 15. Akwai kamfanonin harkokin noma bakwai. Shida kuma kamfanonin gine-gine.

Akwai kuma na harkokin kayan lantarki da gas da sadarwa da sauran su.

JERIN SUNAYEN KAMFANONIN SU 34

Rensource Distributed Energy Limited

Sumo Steels Limited (Pipeline division)

CDK Integrated Industries Limited

Lafarge Africa Plc

Edimara Properties Limited

Wacot Rice Limited

Tribute Lifestyle Global Concept Limited

Owerri Mall Development Company Limited

Power Gas Delta Innovations Limited

Asaba Mall Development Company Limited

Triton Aqua Africa Limited

ATC Nigeria Limited

Confluence Metal Fabricating Company Limited

Unicane Industries Limited

Grand Pela Hotels and Suites Limited

Globus Resources Limited

Karshi Agro Farms Limited

Obu Cement Nigeria Limited

Txtlight Power Solutions Limited

Sumo Steels Limited

Skretting Nigeria Limited

Dharul Hijra Fertilizer Company Limited

Olam Hatcheries Limited

Jabi Mall Development Company Limited

Harvestfield Industries Limited

Power Gas Global Investment Limited

Polar Petrochemicals Limited

Hayat Kimya Nigeria Limited

Kalambaina Cement Company Limited

Dangote Sinotrucks West Africa

Royal Pacific Group Limited

Wells-Hosa Greenhouse Farms Limited

Honeywell Flour Mills Nigeria Plc

Share.

game da Author