Tsoffin editocin jaridar Daily Trust, Nasir L Abubakar da Lawal Danjuma Adamu sun kama aiki a jaridar Dateline dake wallafa labarai a yanar gizo.
Editocin biyu sun yi murabus daga jaridar Daily Trust a cikin wannan shekara ta 2020.
Shugaban Jaridar Dateline, Fateema Bello ce ta sanar da wannan babban Kamu da jaridar tayi a wata takarda da ta rabawa manema labarai ranar Talata.
Fateema ta ce jaridar ta yi matukar farin cikin shigowar wadannan gogaggun ‘yan jarida jaridar Dateline sannan kuma jaridar na yi musu maraba da zuwa.
” Nasir Lawal da Lawal Adamu gogaggun ‘yan jarida ne da suka shafe shekara kusan 30 ana fafatawa da su a aikin jarida. Kwarewar su da sanin dabarun aikin jarida babban abin alfahari ne a garemu a Dateline.” Inji Fateema.
Fateema ta kara da cewa editocin biyu za su taimaka wajen tabbatar da manufofin jaridar wanda ya hada da yin labarin masu zurfin bincike da fayyace gaskiya tsantsagwaranta a koda yaushe.
Shi dai Nasir Lawal ya fara aikin jaridar sa ne tun a shekarar 2004. Yayi karatu a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna Polytechnic da jami’ar Bayero dake Kano. Bayan haka ya samu lambobin yabo da karramawa da dama a lokacin aikin sa da ya shafe kusan shekara 30 yana yi. Ya yi murabus daga Daily Trust yana rike da mukamin Babban Editan Jaridar.
Shi kuma Lawal Adamu, wanda shima tsohon ma’aikacin Daily Trust ne, kafin ya yi murabus, shine editan Jaridar da ake bugawa a duk Karshen Mako, wato ‘Saturday Trust’ baya ga wasu mukamai da ya rike da kuma gogewar sa a aikin jarida.
Yayi karatu a jami’ar Usman Danfodiyo dake Sokoto.
Nasir Lawal zai hau kujerar mukamin Shugaba kuma babban Editan jaridar Dateline, shi kuma Lawal Adamu, Babban Editan labarai na yau da Kullum.
Discussion about this post