Jami’an kwastam da ke aiki a jihar Kebbi sun kama wata mota dankare da bindigogi da harsashi a Yauri.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Joseph Attah ya sanar da haka ranar Litini a Abuja.
Attah ya ce ma’aikatan hukumar dake aiki a bakin ruwa ne suka kama mota.
Ya ce an boye wadannan bindigogi da harsasai ne a cikin budunan shinkafa. An samu bindigogi 73 da harsasai sama da 800.
An kama mutum uku dake da hannu wajen shigo da wadannan makamai sannan kuma Attah ya ce ana ci gaba da yin bincike akai.
Attah ya ce hukumar za ta ci gaba da maida hankali a aiyukkanta musamman wajen ganin ta toshe duk wata kafa da ake bi wajen shigo da makamai kasar nan.
Ya kuma yi kira ga mutanen dake zama kusa da iyakokin ƙasa da su rika taimaka wa hukumar kwastam da bayanan da za su taimaka wajen kamo ‘yan sumogal da masu safarar kayayyaikin da aka hana shigowa da su irin haka.