Hukumar Babban Birnin Tarayya, Abuja ta bayyana cewa zuwa ranar Litinin an kididdige jami’an kula da lafiya na yankin 476 ne su ka kamu da cutar korona, yayin da cutar ta yi sanadiyyar ajalin likitoci hudu wadanda ba su cikin wannan lissafi.
Sanarwar ta kara da cewa mutuwar baya-bayan nan ta wata mata ce jami’ar kula da lafiya.
Sanarwar ta ce wadanda su ka kamu da cutar sun hada ma’aikatan kiwon lafiya, nas-nas, jami’an kula da dakin gwaji, direbobi da ma’aikata na yau da kullum.
Sanarwar ta ce wannan cuta ta ci rayukan likitoci hudu, daga cikin su kuma wata mata ce ta rasu a baya-bayan nan.
Kakakin Yada Labarai na Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Muhammad Bello ne ya fitar da wannan sanarwa, ranar Talata a Abuja.
Ya kara da cewa duk da wannan kaluble da ake fuskanta, dukkan asibitocin Abuja a bude su ke ana ci gaba da ayyukan kula da marasa lafiya tsawon sa’o’i 24.
“Tsawon mako daya kenan rabon da a samu bayanin mutuwar wani majiyyaci sanadiyyar cuutar korona.
“Ya na da kyau jama’a su sani cewa wannan yawan kamuwar jami’ai da cutar korona, ko kadan bai rage aikin gudanarwa da kula da marasa lafiya da ake yi a Abuja ba.’
Idan ba a manta ba, mun buga labarin yadda korona ta kashe likitoci 20 cikin mako daya a fadin kasar nan.