In Dai Har Irin Su Abdullahi Abbas Sune Shugabanni A Kano Da Arewa…! Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai!

Assalamu Alaikum

Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun! Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun!! Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun!!!

‘Yan uwa na masu daraja, wallahi, Allah ya sani, kuma shine shaida, tun da na kalli wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen yada labarai na zamani, wato soshiyal midiya, na shugaban jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano, wato Abdullahi Abbas, kawai sai na rude, hankalina ya tashi, na shiga damuwar da ban taba shiga irin ta ba! Ace wai wannan mutum shugaba ne a arewa, ace wannan mutum magidanci ne, da yake da iyali, mata, da yara!!

Abdullahi Abbas ya fito yana ashar, da zagi, da tsinuwa, da la’ana, da zuga ‘ya ‘yan mutane suyi tashin hankali, su kashe mutane, su zubar da jini, duk da sunan adawar siyasa tsakanin APC da PDP. Sun lalata yaran talakawa, sun mayar da su mashaya, sun mayar da su ‘yan daba, sun mayar da su ‘yan ta’adda, amma su sun boye nasu yaran, suna ta basu ilimi. Idan sun wuce kuma yaran nasu sune za suci gaba da jagorantar wadannan yara, ‘ya ‘yan talakawa, da suka lalata wa rayuwa.

Nayi imani da Allah, wannan bidiyo da ke yawo, mutane da dama sun gan shi, amma da yake wannan mutum dan jam’iyyah mai ci ne, dan gata ne, babu abunda za’ayi, kuma babu wani matakin da za’a dauka!

Kullun mu ‘yan arewa, muna ta yaudaran kawunan mu, muna ta munafuntar kawunan mu, muna ta surutan banza, muna ta yin taruruka na shan shayi a watse, muna ta yin tarukan karawa juna sani na karya, muna ta koke-koke da munafunce-munafunce, muna ta yin rubuce-rubuce na neman mafita, da kuma kokarin magance ko kuma kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi yankin mu, amma duk mun manta cewa, mun fa bar jaki ne muna ta dukan taiki!

Dalilina na fadar wannan magana shine, to ta yaya zamu tsaya, muna munafuntar kawunanmu, munyi shiru akan kazaman ‘yan siyasar da ke lalata rayuwar matasanmu, sun mayar da su ‘yan daba, sun mayar da su ‘yan ta’adda, sun mayar da su marasa imani, marasa kishin addininsu, marasa kishin al’ummarsu, marasa kishin kasarsu, marasa kishin yankinsu, marasa kishin manyansu, marasa kishin na gaba da su da iyayensu? Na rantse da Allah, wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi kadai, ina mai shaida maku cewa, idan bamu fara daukar mummunan mataki akan irin wadannan ‘yan siyasar ba, idan bamu fara yin maganinsu ba, idan bamu fara nuna masu cewa da gaske muke yi ba, to wallahi babu yadda za’a yi mu iya magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin mu!

Yanzu domin Allah, shi wannan mutum, wato Abdullahi Abbas, da ya tara ‘ya ‘yan talakawa, miskinai, yana yi masu irin wannan mummunar lakca, don Allah ina nasa ‘ya ‘yan suke ne? Don girman Allah zai iya tara ‘ya ‘yansa ya isar masu da irin wannan sako, domin su tafi su aiwatar da shi akan wasu? Shin domin Allah irin yadda yake zuga wadannan matasa suyi ta’addanci, zai so nasa yaran su zama ‘yan ta’adda? Me yasa har kullun ake ta cutar da mu, ake ta cutar da matasan mu na arewa, ake ta mayar da mu baya, da sunan siyasa ko da sunan adawar siyasa, amma mun yi shiru, bamu cewa komai? Ga abubuwan da ke jawo muna rikice-rikice da tashin hankali da zubar da jini da rashin zama lafiya, kai da dukkanin matsalolin rashin tsaro, amma saboda munafunci irin namu, mun yi shiru, bamu cewa komai, sai kace wadannan wawayen kazaman ‘yan siyasar sun fi karfin mu ko sun fi karfin kowa?! Kuma don rashin sanin ciwon kai, idan wani ya fito yayi magana, ya fadakar, ya jawo hankalin hukumomi da manya, amma sai ka ga wani wawa shi kuma can, wai yana cewa baka kyauta ba, ai ba haka ya kamata kayi ba!

Shi mai wannan irin magana, yana fada maka ita ne, saboda ba’a saci dan uwansa ko ‘yar uwarsa ba, ko ba’a saci dan sa ko ‘yar sa ba, ko kuma ba’a yiwa uwarsa ko ‘yar sa ko matar sa fyade yana kallo ba, shi yasa yake wannan magana!

Don Allah, don Allah, don Allah ina jami’an tsaron Najeriya suke ne? Don Allah, don Allah, don Allah ina shugaban kasa Muhammadu Buhari yake ne? Don Allah, don Allah, don Allah ina gwamnonin mu na arewa suke ne? Don Allah, don Allah, don Allah ina dukkanin manyan jihar Kano suke ne, da matasan jihar Kano, da manyan arewa da matasan arewa da malaman arewa da sarakunan arewa, kai da duk wani mai fada aji a arewa, ina kuke ne don girman Allah, a lokacin da wannan mutum, Abdullahi Abbas yake wadannan maganganu? Shin kuna nufin ku fada mani cewa yanzu yankin mu na arewa mai albarka ya zama wurin da ko wane irin wawan mutum zai fito yayi abunda ya ga dama, ya fadi maganganun da yaga dama, wadanda zasu iya zama sandiyyar tarwatse arewa, ba tare da an taka masa burki ba? Ba tare da an dakatar da shi ba? Ba tare da an dauki mataki a kan sa ba? Ina mai tunatar da ku cewa fa, wallahi irin wannan yin shiru akan lamurra da muke yi, tare da kyale kowa yayi abunda ya ga dama, da nuna halin ko-in-kula, shine ya kai mu halin da muke ciki a yau. Ya kamata mu san wannan!

Ya ku manyan arewa, ku sani, wallahi muna matukar ganin girman ku, tare da baku daraja, da son ku da kaunar ku, a matsayinku na manyanmu kuma iyayenmu, shi yasa bamu daukar doka a hannun mu game da irin wadannan al’amurra. Sannan kuma mun san cewa dokar kasar mu bata yarda mutum ya dauki doka a hannunsa ba, kasancewar akwai hukuma. Amma idan har kun kasa, kuma hukuma za ta bamu goyon baya tare da izini, to wallahi ina mai tabbatar maku cewa mu a shirye muke da muyi maganin duk wani shedani, dan ta’adda, da ikon Allah kuma da buwayarsa! Kuma a shirye muke da mu yi maganin duk wasu wawaye, kazaman ‘yan siyasar da ke lalata muna rayuwa, kuma su lalata rayukan matasanmu, alhali su ba zasu taba yarda ‘ya ‘yansu suyi irin abun da suke zuga ‘ya ‘yan wasu suyi ba!

Kuma wannan magana da nike fada, kar wani ya dauka da wasa nike yi, ko kuma ba’a nike yi. Ina mai rantsuwa da Allah da gaske nike yi, kuma babu wasa ko ba’a a cikin ta!

Ya kamata jama’ah su fahimci cewa fa mungaji, mungaji, mungaji da irin wannan cin mutunci da ake yi muna, da irin wannan wulakanci da ake yi muna. Ya isa haka nan!

Kullun muna ce maku ya kamata mutanen kirki, na kwarai su shiga siyasar nan, domin idan basu yi ba, to mutanen banza, ‘yan tasha, marasa da’a da kishi da tarbiyyah, sune zasu shige ta, su mamaye komai, kuma su zama shugabannin ku. To yanzu ga irin ta nan, wannan shine muke ji maku tsoro, ga shi nan ‘yan iska, ‘ya ‘yan banza, suna kusa ga su mamaye siyasar. Kuma da an wayi gari duk sune shugabannin ku, to wallahi kun shiga uku, kun lalace!

Saboda haka ya zama dole, kuma wajibi mu shiga taitayinmu. Ni na riga na gaya maku, ba zamu taba rungume hannuwa, muna kallo ana cutar da yankin arewa da Najeriya ba muyi shiru. Da ikon Allah sai kowa ya gane na kwarai, sannan sai kowa ya gane mugu. Idan kuma muka gane su, to zamu ci gaba da bayyana maku cewa yanzu me ya kamata muyi da su da ikon Allah!

Wassalamu alaikum

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun Imam a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author