HIMMA DAI MATA NOMA: Yadda masu garkuwa su ka hana mu zuwa gonakin mu –Inji Safiya

0

Wata mata mai suna Safiya Yahaya, mai shekaru 48 da ‘ya’ya biyu, ta bayyana yadda ta shekara 20 ta na noma a jiihar Kogi.

Sai dai kuma a yanzu, Safiya, wadda ta shaida wa wakilin mu cewa ta na noma shinkafa, rogo da kasshu, ta ce abin ya canja, domin masu garkuwa da mutane jira kawai su ke yi su ga mai noma a gona, su yi awon-gaba da shi.

“Na fara noma tun a cikin gonar iyayen mu ta gandu, amma daga baya da mu ka koma cikin gari, muka bar kauye, sai na sayi gona ta, ta kai na, wadda na ke nomawa. Wannan gonar za ta kai hekta biyar.

“Kamar yadda ka yi tambaya, wani lokaci mukan fuskanci matsalar samun irin shukawa. To amma ni duk da mu kan samu a wani lokaci daga shirin ‘Anchor Borrowers’, ina rage irin da zan shuka a shekara mai zuwa daga cikin amfanin gonar da na girbe a wannan shekara.

“Sannan kamar yadda ka yi tambaya, ni ba ido-rufe na ke noma ba. Sai na zabi kasa mai albarkar noma tukunna. Akwai kasa mai tsandauri, wadda ko ka noma shinkafa a wurin asara za ka yi. Akwai kuma amfanin gonar da idan ka shuka shi inda

“Harkar noma din nan da ake ganin ta, akwai rufin asiri a cikin ta. Domin da amfanin gonar da na noma na ke biyan dukkan dawainiyar gida da sauran bukatu na.

“Gona ta mai fadin hekta biyar ce, kuma tabbas ina amfani da kayan noma na zamani, amma kamar irin wadanda ba su fi karfin mata su sassafa su ba. Wato irin su cakarkara kenan.

“Na sayi daya, tawa ce, kuma Ma’aikatar Gona ta ba mu lamuni, za ka biya wani kaso na kudin kafin ka karba.

Safiya ta ce harkar shinkafa ana samu, kuma wani lokaci idan aka yi ambaliya, to akan tafka asara. Ta ce a bana har ta girbe shinkafa tan 20, amma ba a kammala aikin ba tukunna.

Ta kan kwashi kayan abincin da ta noma ta sayar da wani kaso, wani kason kuma a rika ci a gida.

Ta ce a Babbar Kasuwar Kogi ta ke sayar da kayan gonar ta.

Ta nuna rashin jin dadin cewa wani tallafin gwamnati bai taba zuwa hannun ta ba. Sannan kuma ko a kungiyance idan aka kawo wani abu, to maza kan nuna musu bambancin fifiko, sai sun fara rabawa tsakanin su, sannan su ke bai wa mata.

Da ta ke magana a kan rashin tsaro, Safiya ta bayyana irin mummunan halin da su manoma ke ciki a yankin su.

“Ka ga a okacin da kasar nan ke kwance lafiya, mukan fita zuwa gona karfe 5 na asubahi. Karfe 10am na safe kuma mun dawo. To amma hakan ba zai taba yiwuwa ba a halin yanzu. Ka na fita masu garkuwa za su damke ka, su yi gaba da kai.

“Yanzu lamari ya lalace, mutum ba zai iya fita shi kadai ba. Sai dai mu jira a yi gangami a fita a cikin gungun jama’a, kuma a dawo tare lokaci daya. Wannan kuwa matsala ce. Domin idan kai ka shirya fita un karfe 8 na safe, to wasu kuma sai karfe 10 na safe su ke da lokacin fita. Ka ga tilas sai an jira su kenan.”

Safiya ta yi fata da rokon bukatar tallafin da ake bai wa manoma, domin ita ma ta kara, bunkasa harkokin noman ta.

Ta ce mata da yawa na bukatar irin wannan tallafi, domin kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a yankin su, duk mata ne ke noma shi.

Share.

game da Author