Babbar Kotun Tarayya da ka Abuja ta ki amincewa da bukatar Gwamanatin Najeriya domin haka Mohammed Abacha shigar da kara, inda ya yi ikirarin cewa rigiyar danyen man fetur mai lasisi OPL 245, ta sa ce, halak malak.
Shi dai Mohammed Abacha ya maka Gwamnatin Tarayya kotu, tare da kamfanin Shell Exploration anda Production Ltd da kuma Nigeria Agip Exploration Company, dukkan su kamfanonin da ke hako danyen mai a Najeriya.
Ita dai gwamnatin tarayya ta yi kokarin hana Mohammed,dan tsohon Shugaba na mulkin soja ikirarin mallakar rijiyar danyen man, mai lamba 245.
Sauran wadanda Mohammed Abacha ya maka kotu, sun hada da Ministan Harkokin Fetur, Shell Nigeria Ultra-Deep Ltd da kuma tsohon ministan fetur, Dan Etete.
Mohammed Abacha ya shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/201/2017, inda ya ke ikirarin cewa ai shi ne ya fi kowa hannun jari mai kauri a rijiyar danyen mai ta Malabu Oil and Gas Ltd.
A hukuncin da ta zartas, Mai Shari’a Binta Nyako ta ce kotu na da ‘yancin tsayawa ta saurari karar da Mohammed Abacha ya shigar wadda ke da nasaba da danyen man fetur da gas.
Binta ta ce Gwamnatin Najeriya da sauran wadanda Mohammed Abacha yam aka kotu, ba su da ikon hana kotu sauraren karar da dan na marigayi Abacha ya shigar.
Sannan ta ce Mohammed Abacha na da ikon hadawa da Ministan Harkokin Mai na Najeriya na yanzu duk ya maka kotu kamar yadda ya yi, domin a bisa doka, za a iya maka shi kotu, shi ma kuma zai iya maka wani kotu idan ta kama.
MALABU OPL 245: Rijiyar Da Ta Fi Kowace Rijiya Yawan Danyen Mai Afrika:
Ita wannan rijiya, wadda ke da lasisi mai lamba OPL 245, an kiyasta cewa ta fi kowace rijiyar danyen mai zurfi da yawan ruwan mai kwance a karkashin kasa.
An kiyasta akwai danyen mai kwance a karkashin ta fiye da ganga bilyan tara (9). Ministan Fetur Dan Etete ne ya bayar da lasisin mallakar rijiyar ga kamfanin Malabu, a cikin 1988, a lokacin Etete din ne Minista.
A lokacin Mohammed Abacha ne ke da kashi 50 bisa 100 na jarin kamfanin amma ta hannun sunan bogi, na wani Kwekwu Amafegha, wanda bagaraswa ce, babu wani mai sunan.
Daga baya sai Etete ya yi ikirarin cewa ai shi ne ya mallaki kamfanin na Malabu, domin hukumar gudanarwar kamfanin sun mallaka masa shi.
Sai dai Mohammed Abacha ya karyata Etete, ya ce karya ya ke yi, babu lokacin da aka yi wannan yarjejeniyar.
An dai bayar da rijiyar mai lamba 245 a zamanin mulkin Sani Abacha. Shi kuma Etete ya yi ikirarin mallakar rijiyar bayan mutuwar Abacha.
Mohammed Abacha kuma a yanzu ya ce har yanzu shi ke da kashi 50 bisa 100 na jarin kamfanin na Malabu, wanda babu mai yawan jari a ciki kamar sa.
Markabun OPL 245 Cikin 2011:
An sayar da rijiyar mai lamba OPL 245 ga kamfanin Shell da Eni cikin 2011. An biya dala bilyan 1.1, amma fiye da rabin kudaden su ka shiga aljihun Dan Etete, aka yi ta jidar kudaden ana bayarwa cin hanci ga jami’an gwamnatin Najeriya da na Shell da Eni.
Wannan harkalla ta janyo an yi ta kwatagwamgwamar shari’a a Ingila, Najeriya da kuma Italiya.
Mai Shari’a Binta Nyako ta aza ranar 9 Ga Maris, 2021 fara shari’a.
Gada-gada Da Harkallar Cinikin Rijiyar Malabu Oil 245
HARKALLAR MALABU: AA Oil, da ya karbi dala miliyan 520 ya gurfana a kotun Italiya
Wani dan gada-gada mai suna Abubakar Aliyu, ya gurfana a gaban wata kotun kasar Italiya da ke burnin Milan.
An ce Aliyu shi ne ya rika zama wani gogarman gada-gadar wasu manyan jami’an gwamnatin Goodluck Jonathan suka rika amfani da shi ya na karbar musu makudan milyoyin daloli.
Kotu na ci gaba da sheka masa ruwan tambayoyi dangane yadda aka karkatar da dala biliyan 1.1 daga kamfanin harkar main a Shell da Eni, harkallar da aka ce a tarihin hada-hadar mai ba a taba yin kamar ta ba a fadin Afrika.
MA’ANAR HARKALLAR MALABU: Ita ce wata karimtsa-da-rimatson cuwa-cuwar zunzurutun kudade har dala bilyan 1.1 da kamfanonin hakar danyen main a Shell da Eni suka yi, tare da hannu da hadin bakin yin amfani da asusun ajiyar kudaden gwamnatin tarayyar Najeriya da dama.
An yi wannan karimtsa-da-rimatso ne a lokacin da Dan Etete ya na Ministan Harkokin Man Fetur na Najeriya. Kuma an tabbatar da cewa ba a taba yin harbat-ta-Matin harkalla kamar wannan ba a kamfanin Shell da Eni a fadin Afrika.
Daga cikin wasu asusun ajiya wanda Dan Etete ne kadai ke da hannu da ikon cirar ko da kwandala daga ciki ne aka rika rorar kudade ana zurarawa cikin asusun ajiyar kudi na dan gaga-gada Abubakar Aliyu, wanda aka fi sani da AA Oil.
AA Oil shi ne ke da wani katafarfen gida mai kallon otal din Hilton a Abuja. Gidan ya na kuma jikin farkon titin Gana Street da ke Maitama, Abuja. Ya na daya daga cikin kantama-kantaman gidajen alfarma a Abuja.
KARIMTSA-DA-RIMATSO
An ce an zurara har Dala milyan 520 cikin asusun sa.
Fadi-tashin binciken da aka rika yi ne aka gano cewa AA Oil fa gada-gada ce ya ke yi wa wasu jami’an gwamnati, ba harkar gaban kan sa ba ce.
A cikin 2011 ne Goodluck Jonathan ya bada iznin ya cire kudaden a matsayin kudin biyar farashin Rijiyar Mai wadda ke da lamba OPL 245, daya daga cikin manyan rijiyoyin man da suka fi albarkar danyen mai kwance a karkashin su.
Da farko Shell da Eni sun nuna cewa su ba su ma san da wannan harkalla ba, ba su ci zomo ba, kuma ba a ba su ratayar ko da fatar zomo ba. Cewa suka yi ba su san kudaden a hannun Etete da ‘yan koren sa za su koma ba.
Sai dai kuma wasu hujjoji da PREMIUM TIMES ta mallaka, sun tabbatar cewa karya Shell da Eni ke yi, da su aka kaso zomo kuma da su aka gasa shi, sannan da su aka cinye naman sa.
A zaman yanzu da ana ci gaba da gurfanar da Shell, Eni, Etete, AA Oil da wasu jami’ai da dama a wata kotun Italy da ke birnin Milan.
A ci gaba da shari’ar da aka gudanar a yau Laraba da safe, masu gabatar da kara sun sanar wa Mai Shari’a cewa wani lauyan kasar Italy wanda ya ce shi ne lauyan Abubakar Aliyu mai AA Oil, ya kai musu ziyara jiya Talata inda ya tambayi a sake daga masa kafa domin a dan kara jinkirta shari’ar.
Amma kuma wani hamshakin lauya wanda ke aiki a Kamfanin Lauyoyin Barnaby Pace of UK Global Witness, wanda ya halarci zaman kotun ko a yau Laraba da safe, ya ce lauyan bai je kotu ba a yau, kuma bai aiko da dalilan rashin zuwan sa kotun ko da a rubuce ba.
KALLO YA KOMA KOTUN BIRNIN MILAN
Yayin da aka fara gabatar da bayanai a gaban mai shari’a, Aliyu ya tabbatar da cewa ya samu bayanan dukkan caje-cajen da ake yi masa.
Amma kuma ya ce shi zai iya kin amsa tuhume-tuhumen don kada gina wa kan sa rami kuma ya rufta da shi a gaban alkalin Italiya.
Sai dai kuma daga bayan PREMIUM TIMES ta samu tabbacin cewa lauyan da ke kare AA Oil ya halarci kotun a birnin Milan a yau Laraba.
Haka kuma ita ma gwamnatin Najeriya akwai lauyan da ta tura da ke sauraren ba’asin bayanai kuma ya ke bibiyar shari’ar a cikin kotun.
Aliyu AA Oil ya nemi a kara jinkirta masa lokaci, ta yadda sabbin lauyoyin sa za su yi nazarin yadda tuhume-tuhumen da ake yi masa suke, sannan kuma su san irin kamun ludayin da za su yi idan an fara sa-in-sa a gaban mai shari’a.
PREMIUM TIMES ta gano cewa masu gabatar da kara sai kwanan nan suka aika wa AA Oil sammacin tuhume-tuhumen da ake yi masa.
To a yau Laraba mai shari’a ya amince ya jinkirta wa Aliyu har zuwa lokacin da lauyoyin sa za su yi nazarin takardun tuhume-tuhumen da ake yi masa. Ya ce caje-cajen da ake yi masa masu nauyi ne matuka, su na da bukatar lauyoyin sa su je su yi nazari.
Mai Shari’a ya ce zai bayar da ranar da za a dawo a ci gaba da shari’a.
Da farko an jinkirta gurfanar da AA Oil a kotu ne, saboda jami’an EFCC a Najeriya sun ce shi da sauran wadanda ake zargi duk sun cika wandon su da iska, sun tsere.
Sai a cikin watan Maris, 2013 ne EFCC ta sake buga musu sabbin caje-caje, shi da sauran wasu, har da Mohammed Adoke, tsohon Ministan Shari’a na zamanin mulkin Goodluck Jonathan da ministan harkokin man fetur na lokacin, Dan Etete. An tuhume su da hannu wajen yi wa dalar Amurka bilyan daya da milyan dari daya kurbar ruwan shayi.
Duk da cewa Mohammed Adoke ya sha musanta cewa ba da shi aka ci kudin ba. Amma kuma tun da ya fice daga Najeriya, har yau ya ki dawowa domin ya amsa tuhumar da ake yi masa, ballantana ya kare kan sa.
Mai Shari’a ya ce zai bayar da ranar da za a dawo a ci gaba da shari’a.