Gwamnatin Tarayya ta kara yawan yawan matasa masu cin moriyar Shirin N-Power daga mutum 500,000 zuwa Milyan 1.
Ministar Ayyukan Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq ce ta bayyana haka, a lokacin da ta ke taron manema labarai, ranar Talata a Abuja.
Shirin N-Power na cikin shirye-shiryen ayyukan inganta rayuwar al’umma (SIPs) da wannan ma’aikatar ke sanarwa.
Shiri ne na ka-yi-aiki-a-biya-ka da Gwamnatin Shugaba Buhari ta kirkiro cikin 2016.
Ya fi maida hankali wajen samar wa matasa aikin yi a fannonin gona, kiwon lafiya, ilmi da kuma bangaren tara kudaden haraji.
An fara Rukuni na A da matasa 200,000 cikin 2016. Sai Rukuni na B da matasa 300,000. An fara shi cikin Augusta, 2018.
An sallami wadannan kurunnai na A da Ba cikin Yuni, 2020, domin bada damar sake daukar wasu sabbi.
Yayin da a yanzu shirin ke karkashin Ma’aikatar Harkokin Jinkai da Agaji, Sadiya ta ce an fadada shirin a cikin tsarin GEEP da Babban Bankin Najeriya ya shigo da shi,
Sadiya wadda a lokacin ganawar ta da manema labarai ta karanto da jero wasu muhamimman ayyukan da ma’aikatar ta ta yi, ta ce an samu nasarar gudanar da ayyukan bisa kokarin an tabbatar da muradin Shugaba Buhari na samar wa mutum milyan 100 aikin yi, nan da shekaru 10.
“Saboda Shugaba Buhari na son ganin muradin sa na ganin mutum milya 100 sun samu aiki nan da shekaru 10,000, ya kara ma’aikatan N-Power daga su 500 000 zuwa milyan 1. Ya kara na shirin GEEP zuwa mutum milyan daya. Yayin da shirin ciyar da yara ‘yan makaranta na nan mutum milyan biyar na amfana da shi.”
Sadiya ta kara da cewa Rajistar Marasa Galihu da ke amfana ta karu daga gidaje milyan 2.8 zuwa gidaje milyan 3.7.
Dangane Da Korafin Raba Tallafin Kayan Abinci Lokacin Zaman Korona:
Minista Sadiya ta ce gwamnon aka ba kayan abincin tallafin gwamnatin tarayya da na manyan ‘yan kasuwa da kamfanoni na CACOVID-19 domin su raba.
“Wasu Gwamnonin sun raba na su, wasu kuma su ka kinshe na su a rumbuna, saboda wasu dalilai na daban da su kadai su ka sani.”
Idan ba a manta ba, irin wadannan rumbunan ajiyar da aka kimshe kayan abincin a wasu jihohi ne aka rika fasawa, ana kwasar ‘ganima’ a lokacin tarzomar #EndSARS a wasu jihohi.