Gwamnatin Tarayya ta amince a kashe naira bilyan 117 wajen gyaran manyan titina

0

A taron Majalisar Zartaswa da aka gudanar Laraba a Fadar Shugaba Muhammadu Buhari, an amince a ware makudan kudade naira bilyan 117 domin ayyukan gyaran manyan titina a fadin kasar nan.

Ministan Ayyuka, Babatunde Fashola ne ya bayyana wa manema labarai haka, bayan tashi daga taron a Villa, Fadar Gwamnatin Najeriya.

“An ware naira bilyan 18.9 domin gyaran titinan da su ka hada da gadoji a Kano, Kaduna da Jigawa a kan kudi naira bilyan 8.787.

Sai kuma gyaran titin Omo zuwa Umulokpa a Jihar Enugu, kan kudi naira bilyan 1.712.

Akwai gyaran titin Oye zuwa Oranta a Jihar Anambra kan kudi naira bilyan 2.504.

Akwai gyaran gadar Okpolo akan hanyar da ta hada Jihar Benuwai da Jihar Cross River a kan kudi naira bilyan 1.057.

Sai gyaran gadar kan hanyar Bida zuwa Zungeru, kan kudi naira bilyan 1.022.

Sauran kudaden za su shige wajen gyaran gadoji a jihohin Abia, Enugu, sai Gadar Challawa da ke cikin Karamar Hukumar Kumbotso a jihar Kano a kan naira bilyan 2.787.

Sauran kudi naira bilyan 98.078 kuma sun hada da na aikin gyaran titin hanyar Rijiya zuwa Gusau kan naira bilyan 7.799, hanyar Jeha zuwa Sanagi zuwa Gumi a Jihar Kebni kan naira bilyan 31.5, hanyar Koko zuwa Mahuta a jihar Kebbi kan kudi naira bilyan 19.713 da wasu hanyoyi a Katsina, Anambra, da hanyar Bichi zuwa Kano kan kudi naira bilyan 8.384 ita kuma.”

Fashola ya ce wasu daga cikin wadannan titinan an dade da yin watsi da aikin su, shekaru dama da su ka wuce.

Share.

game da Author