Babban Daraktan Hukumar Bada Katin Shaidar Dan Kasa (NIN), ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ba za a kara wa’adin yin katin dan kasa ga kowa ba.
Duk kuwa da sukar bada makonni biyun da aka yi cewa kowa ya tabbatar ya jona lambobin wayar sa da lambar katin sa na dan kasa, ita dai gwamnatin tarayya ta ce ba za ta kara wa’adin ko kwana daya ba.
Shugaban Hukumar Samar da Katin Dan Kasa, Aliyu Abubakar, a wata tattaunawa da ya yi da PREMIUM TIMES a ranar Juma’a, ya ce gwamnati ba za ta kara wa’adin ba.
“A yan zu haka yadda abin ke tafiya, to ba za a iya kara wa’adin ko da rana daya ba. Kada ya kasance mu na korafe-korafe, maimakon haka, mu dauka kawai za mu iya cimma kudirin kammalawa a cikin makonni biyu din.” Inji Abubakar.
“Kamata ya yi sai an kai kwanaki 10 ko ma kwanaki 12 ana yi tukunna, sannan za a iya bijiro da batun a roki gwamnati ta kara wa’adi.”
Karancin wuraren yin rajistar katin dan kasa a fadin kasar nan ya sa ‘yan Najeriya sun shiga soshiyal midiya su na ta sukar sabon tsarin, daga mai tsinuwa, sai mai yin tir, sai masu yin Allah ya isa da Allah-wadai.
Da yawan mutane dai na ganin cewa bai dace a bijiro da tsarin ba, a wannan lokaci da ake shirin hutun Kirsimeti.
Sannan kuma ana ganin wannan shiri zai kara ambaliyar kamuwa da cutar korona, ganin yadda a wasu wurare jama’a sun yi cincirindo, kowa na kokarin a yi rajista, ba tare da kiyaye dokar yin kaffa-kaffa daga kamuwa da cutar korona ba.
Duk da cewa an bayar da lasisi ga wasu ejan-ejan a wasu jihohi domin abin ya yi sauri, ana ganin wa’adin makonni biyu sun yi kadan matuka.
Jihohin da aka bai wa ejan-ejan lasisin yin aikin rajistar dai sun hada Abia, Akwa Ibom, Gombe, Kaduna, Katsina, Kano, Oyo, Ogun, Sokoto,Deta, Ebonyi, Cross River, Adamawa da kuma Zmafara.
An kuma bada lasisin yin rajistar ga NCC, CBN, EFCC, INEC da NPS. Sannan kamfanonin layiin waya irin su MTN, GLO, AIRTEL da 9Mobile duk an ba su lasisin yin rajistar.
Akwai kuma kungiyoyin sa-kai bakwai da su ma aka ba su lasisin yin rajistar.
Sai dai kuma inda markabun ya ke shi ne tun daga 2012 har zuwa 2020, mutum milyan 43 ne kadai su ke da katin dan kasa ko su ka yi rajistar neman mallakar katin dan kasa, a kasa kamar Najriya mai mutum milyan 208.
Dalili kenan ake ganin wa’adin makonni biyu kacal zai haifar da gagarimar matsala, musamman cinkoson jama’a a lokacin da korona ta fi fantsama a kasar nan.
Discussion about this post