Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa gwamnati za ta saka tsoffi cikin shirin inshorar lafiya a kasar nan.
Ehanire ya kuma kafa kwamiti wanda za ta yi aiki da hukumar inshoran lafiya domin shirya irin tsarin da za a saka tsoffin a ciki.
“Daukan wannan mataki zai taimaka wajen girmama da karrama tsoffin da suka dade suna wa ƙasa bauta.
Bincike ya nuna cewa mafi yawan mutane a kasar nan matasa ne sannan adadin yawan tsoffin da ake da su na karuwa kullun.
Hukumar kidaya ta ƙasa NPC ta bayyana cewa adadin yawan tsofaffin da ake da su a kasar nan ya karu daga miliyan 8.7 a shekarar 2013 zuwa miliyan 9.6 a shekarar 2016.
Hukumar na hasashen cewa adadin yawan tsofaffin a Najeriya zai Kai miliyan 20 nan da shekaran 2050.