Ma’aikatar Sadarwa da Bunkasa Tattalin Arziki ta fidda wata sanarwa dake umartar kamfanonin sadarwa, MTN, Glo, Airtel, 9Mobile kada su sake yi wa wani sabon layi rajista.
Ma’aikatar ta ce ta yi haka ne domin ta iya kammala tantance layukan da aka riga aka yi wa rajista a kasar nan da samun cikakken bayanan su wato cikakken bayannan wanda ke da mallakin duk wata layi.
Ma’aikatar ta ce duk kamfamin da aka samu ya karya wannan doka ya kuka da kansa, domin har lasisin sa gwamnati za ta kwace.
Pantami na zawarcin dimbin masu zuba jari a fannonin tattalin arzikin fasahar zamani
Ministan Sadarwa da Bunkasa Tattalin Arziki ta Hanyar Fasahar Zamani, Isa Pantami, ya yi kira ga masu zuba jari a fannonin sadarwa su zabura wajen turereniyar zuba makudan jari wajen bunkasa tattalin arzikin fasashar zamani.
Da ya ke gabatar da lacca a Toron Masu Zuba Jari na ‘Africa Investment Forum, wanda wani taron bayan-bage ne a Taron GITEX a Dubai, Pantami ya ce akwai riba mai tarin yawa, idan manyan masu zuba jari su ka gane lakanin da ke tattare da tattalin arzikin fasahar zamani.
Pantami ya ce a Najeriya akwai kasuwa da yawan bukatun fasahar, akwai yawan dimbin al’umma, sannan kuma ladar da ake biyan lebura ko ma’aikaci ba mai tsada ba ce sosai.
Ya ce zuba jari a fannonin sana”ar tattalin arziki na zamani zai bada damar kusantuwa da mutane sama da milyan 550. Domin Najeriya ce babbar kofar shiga da fita kasashen Afrika ta Yamma da kuma Afrika ta Tsakiya.
“Akwai al’umma milyan 200 a Najeriya da kuma milyan 200 a Afrika ta Yamma da wasu milyan 150 a Afrika ta Tsakiya.
“Zuba jari a Najeriya zai bayar da damar samun hazikan matasa kuma zakakurai masu kyakkyawar kwarawa. Sannan kuma ba su da tsadar dauka aiki kamar sauran kasashen duniya.
“Yan Najeriya da dama sun taka rawa a duniya wajen kirkiro mamhajojin sadarwar fasahar zamani da ake cin moriya a yanzu.
“Dan Najeriya na cikin sahun gaban likitocin duniya da su ka kirkiro maganin riga-kafin cutar korona. Rahotanni sun nuna wannan allurar rigakafi za a iya yin cinikin ta dala bilyan 8 daga nan zuwa karshen 2021.
” An kuma samu wani dan Najeriya ya kirkiro hancin na’urar da ke iya sinsinar cutar korona.
“Tuni har an yi jarjejeniya da kamfanin sufurin jiragen sama na Airbus domin a kirkirar masu wadda za a ranar ka makalawa cikin jiragen su, domin ta rika sinsino masu masu dauke da cutar.
“Wasu manhajoji da ‘yan Najeriya su ka kirkoro sun hada da Hopstop, wadda aka sayar wa kamfanin Apple dala bilyan 1.