Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa rashin daraja da rashin kana’ar zuci ke sa shugaban addini zai yi amfani da ranar Kirsimeti sukutum ya rika ruruta wutar rikici da kiyayya a cikin kasa.
Wannan gargadi ne ga Bishop na Darikar Katolika, Hassan Kuka, wanda gwamnati ta ce maimakon ya yi amfani da ranar Kirsimeti ya yi kiraye-kirayen zaman lafiya, sai ya yi amfani da ranar ya rika zuzuta fitina da raba kan al’ummar Najeriya.
Kukah dai a sakon sa na ranar Kirsimeti, ya bayyana cewa Buhari ba ya komai sai nuna kabilanci, wajen nade-naden sa.
Ya ce “da wani dan Arewa wanda ba Musulmi ne ke mulki ba, kuma ya ke nuna bambanci ko da kadan kyas daga irin yadda Buhari ke yi, ko da kankani ne, to da tuni an kifar da gwamnatin sa, kuma da tuni ana yaki.”
Sai dai kuma a sanarwar da Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya yi, ya bayyana gargadi ga shugabannin addinai su daina furucin hauragiya, wand aka iya haifar da mummunan sakamako.
Kakakin Yada Labarai na Lai Mohammed, Segun Adeyemi, ya fitar da takardar Minista mai dauke da cewa, yayin da shugabannin addinai ke da hakkin fadar gaskiya ga shugabannin da ke kan mulki, to kada ya kasance an lullube wannan gaskiyar a cikin mayafin fushi, kiyayya, raba kan jama’a da kuma kokarin ruruta fitinar rikicin addini.
“Kawo batun juyin mulki a cikin bayanan sa da kuma nuna wani addini a ce ya na tayar da fitina, ba abin alheri ba ne ga shugabannin addinai, musamman a wannan lokaci na hutun Kirsimeti da aka bukatar masu wa’azi su yada kokarin bukatar zaman lafiya da juna.” Inji Lai.
Lai y ace duk mai kiran sauya gwamnati ba ta hanyar zabe ba, ba kiran a yi juyin mullki kadai ya ke yi ba, ya na kira ne har ma a dagula kasa baki daya.
Discussion about this post