Gidan Gonar Kiwon Kaji na CPP, mallakar Gwamnatin Jihar Cross River ya fara sayar wa jama’a dankara-dankaran kajin naira 5,000 a kan naira 1,800 kacal.
Kajin dai ana sayar da su a matsayin garabasar Kirsimeti, domin saukake wa jama’a tsadar rayuwa lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Gwamna Ben Ayade ne ya bayyana fara sayar da kajin a ranar Talata a Calabar, babban birnin jihar, domin saukake wa jama’a tsadar kajin a kasuwanni.
Ya tabbatar da cewa jama’a su kwantar da hankulan su, domin gidan gonar kiwon kajin na CPP, mallakin gwamnatin jihar zai wadatar da kajin ga duk mai bukatar saye a lokacin shagulgulan Kirsimeti.
“A wannan Kirsimeti za mu sayar wa jama’a kaji dankara-dankara a farashi mai rahusa, domin rage masu fama da tsadar da kaji ke yi kasuwa.” Inji
A yanzu dai dankareriyar kazar da ake sayarwa naira 3,000 a Kano, ta kai naira 5,000 ko naira 6,000 a kudancin kasar nan, saboda gabatowar Kirsimeti da shagulgulan sabuwar shekara.
Tuni dai ake ta nuna damuwa da farashin kajin gidan gona a kasuwanni, lokacin Kirsimeti.
Masu kiwon kaji na danganta tsadar kaji a wannan lokacin da tasadar kayan abincin kaji a kasar nan.
Shi ma wani hamshakin mai kiwon kaji a Abuja, mai suna Ubong Ben, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa tsadar kajin na da nasaba da tsadar kayan abincin kaji.
Gidan Gonar Calachika mallakar gwamnatin Cross Rivers dai kamar yadda Gwamna Ayade ya bayyana, ya na kyankyashe ‘yan tsaki 21,000 a kowace rana.
Discussion about this post