Gagarimar matsalar tsaro alamar kasawar iya rike Najeriya ce ga Buhari – Gani Adams

0

Mai rike da sarautar ‘Garkuwan Daular Yarabawa (Aare Ona Kakanfo), Gani Adams, ya fito ya ragargaji Shugaba Muhammadu Buhari a kan matsalar tsaro a kasar nan.

Ya ce gagarimar matsalar tsaron da ake fama da ita, musamman a Arewacin Najeriya a Jihar Katsina, mahaifar Buhari, alamomi ne bayyanannu da ke nuni da cewa Buhari ya kasa iya rike kasar nan, kuma ba zai taba iyawa ba.

A ranar Lahadi ne Gani ya ragargaji Buhari tare da yin tir da sakacin gwamnatin sa kan sace dalibai 333 na Sakandaren Kimiyya ta Kwana a Kankara.

Gani ya ce duk da Buhari ya yi aikin soja har ya kai mukamin Manjo Janar, horon da ya samu dai ya nuna rikon kasar nan a yanzu ya fi karfin sa.

“Abin da ke faruwa a kasar nan ya nuna mu na cikin wani halin komai ka iya kasancewa. Saboda Allah ya za ka dubi idon iyayen yara ka ce masu an sace yaran su 333 a makaranta daya, kuma a lokaci daya. Abin kunya ne ga shugaban da ke bugun kirji cewa shi kadai ne zai iya gyara kasar nan.

“Sace daliban sakandaren Kankara a jihar Katsina, a lokacin da Shugaban Kasa ke hutu a jihar, ai wulakanci ne babba ga Shugaban Kasa. Ga shi kuma ana fama da gagarimin matsalar Boko Haram.”

Ya kara da cewa duk wadannan su na faruwa ne lokacin da tattalin arzikin mu ya durkushe.

“Ni dai ba masanin tattalin arziki ba ne, amma a bisa yadda dalar Amurka ke ci gaba da yi wa naira dukan tsiya, to kowa ya san mun bani mun lalace.”

Gani ya ce tun tuni ya kamata a sake fasalin mulkin Najeriya.

Tun bayan da Boko Haram su ka yi wa manoma 43 yankan rago a Barno da kuma sace daliban sakandare 333 a Kankara ta Jihar Katsina ne Shugaba Buhari ke ci gaba da shan caccaka.

Share.

game da Author