Fafaroma ya yi jimamin kisan gillar manoman shinkafa a Zabarmari

0

Shugaban mabiya Darikar Katolika Pope Francis, ya bayyana alhinin sa kan kisan gillar da Boko Haram su ka yi wa manoma 43 a Jihar Borno.

Fafaroma Francis ya fadi haka ne a jawabin da yake yi na mako-mako wa mabiyan darikan a birnin Vatican dake kasar Italy ranar Asabar din da ta gabata.

” Za mu ci gaba da yi wa Najeriya addu’a saboda kisan da mahara ke yi a kasar babu kakkautawa ya dakata haka.

Fafaroma ya aika da sakon ta’aziyarsa ga iyalan manoman da aka kashe. Ya yi addu’a Allah ya jikan manoman da rahama sannan Allah ya shirya maharan da suke aikata wannan mummunar aiki.

Aƙala manoma 43 aka yi wa mummunan kisa a ƙauyen Zabarmari da ke cikin Ƙaramar Hukumar Jere ta Jihar Borno a ranar Asabar.

A ranar Talata ne Boko Haram bangaren Shekau su ka bada sanarwar daukar alhakin kai hare-haren kisan gillar da aka yi wa manoman su 43.

Sun ce sun yi masu ramuwar gayya ce saboda mazauna yankin na Zabarmari sun kama dan uwan su daya, sun damka shi ga sojoji.

Bayan haka a ranar Laraba Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba za ta nemi wuri ta zauna ta huta ba, har sai ta tabbatar da ta samo hanyoyin da za ta magance wadannan hare-haren ta’addanci da ake yi.

Osinbajo ya ce kisan ba karamin ta’adddanci ba ne, kuma abin ya taba shi, ya taba zuciyar sa kwarai da gaske. Sannan kuma ya ce ya na mika ta’aziyya, alhini da jimami ga iyalan wadanda su ka rasa rayukan su.

Share.

game da Author