Fadar Shugaban Kasa ta yi maraba da sakamakon zaben cike-gurabu

0

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa sakamakon da ake samu daga zabukan cike-gurabun da INEC ta gudanar a ranar Asabar ya nuna cewa har yau dai jam’iyyar APC ce jam’iyya mai farin jini a Najeriya.

Kakakin Yada Labaran Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka, a cikin wata takardar da ya fitar a Abuja, ranar Lahadi.

“Ba mu yi wa wannan yakini da kyakkywan zato da ‘yan Najeriya ke yi mana shi rikon-sakainar-kashi ba. Saboda haka mu na kan jajircewar mu. Ba kuma za mu karya guyawu kasa mu ce mun gaza ba.

“Ba za mu watsa kasa a idanun ‘yan Najeriya wadanda ke godiya da yabawa kan ayyukan da mu ke gudanarwa ba. Musamman ganin halin da tattalin arzikin duniya da na kasar nan su ke ciki ba, sakamakon barkewar cutar korona a duniya.

“Mu na masu godiya kan ta irin yadda su ka yi imani da kokarin da mu ke yi, tare da ba irin gaskata wannan jam’iyya da kuma gwamnatin.

Garba Shehu ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya gode wa shugabancin riko na Jam’iyyar APC, karkashin Mala Buni, sauran ‘yan kwamiti, gwamnoni da dukkan masu ruwa da tsaki.

Yayin da Buhari ke cewa ya gamsu da sakamakon zaben, ya kuma yi kira ta ‘yan jam’iyyar APC su zama tsintsiya madaurin ki daya, kuma a jajirce ainun.

Share.

game da Author