#EndSARS: Buhari ya yi barazanar kwankwatsar wadanda za su tayar da tarzoma wurin zanga-zanga

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa za a nukurkusa duk wadanda su ka tayar da fitina su ka maida zanga-zanga-zangar lumana ta zama tarzoma har su ka tashi hankulan jama’a.

Buhari ya yi wannan jawabi da ya ke bude Taron Shekara-shekara na Babban Hafsan Sojonin Najeriya, ranar Litinin a Abuja.

Ya yi gargadin daidai lokacin da aka dawo da zanga-zangar #EndSARS karo na biyu, wadda aka fara ranar Litinin, a Oshogbo, babban birnin Jihar Osun.

“Za a dankwafar da duk wani tsageranci da tarzomar da aka fake da zanga-zanga aka karya doka ta hanyar tada tarzoma.” Haka Buhari ya bayyana ranar Litinin a Abuja.

Da ya ke bude taron kai-tsaye daga ofishin sa, Buhari ya jinjina wa sojoji dangane sa yadda su ka samar da tsaro a kasa baki daya, a lokacin da zanga-zangar #EndSARS ta rikide zuwa tarzoma.

Ya ce gwamnatin sa na maraba da bai wa kowa ‘yancin yin zanga-zangar jerin-gwano, ba tare da karya doka abin ya rikide tarzoma ba.

“Amma abin takaici, wasu batagari sai su ka fizge akalar zanga-zangar #EndSARS, su ka mayar sa ita tarzomar da ta haifar da dimbin asarar rayuka da sukiyoyi masu dimbin yawa a garuruwan kasar nan.”

Buhari ya bayyana shekarar 2020 cewa shekara ce mai cike da kalubale musamman fantsamar annobar korona, wadda ta gurgunta tattalin arziki kasa da ma duniya baki daya.

Kafin Buhari ya gama jawabin sa, wanda ya rika jinjina wa sojojin Najeriya, Ministan Tsaro Magashi da Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai duk sun yi jawabai.

Kada Ku Yi Jikara Ko Dari-darin Kwankwatsar Batagari – Jargadin Sufeto Janar Adamu

Kafin wannan umarni da Buhari ya bayar, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga rahoton cikin Nuwamba, inda Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Muhammad Adamu, ya ja kunnen ‘yan sanda cewa kada su yi jikara, dari-dari ko sassaucin kwankwatwar duk wasu batagari a kasar nan.

Adamu ya yi wannan hargadi a ranar Alhamis a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Adamu ya ce ya je Ibadan ne domin ya kara wa ‘yan sandan jihar kwarin guiwa, bayan jikin su ya yi sanyi sakamakon hare-haren da batagari su ka rika kai masu lokacin da tarzomar #EndSARS ta dagule.

“Ku rika mutunta jama’a bisa yadda tsarin dokar kasar nan ya tanadar. Amma kada ku sassauta wa batagari.

“Duk abin da zai same ku matsawar ku na bisa kan aikin ku ne, to mu na bayan ku.” Inji Sufeto Janar Adamu a wurin yi wa ‘yan sandan jihar Oyo jawabi.

Leye Oyebade, wanda shi ne Mataimakin Sufeto Janaral, mai kula da bincike da tsare-tsare, ne ya yi wa Sufeto Janar Adamu rakiya zuwa wannan rangadi a jikin har Ibadan.

Ya yaba wa jami’an ‘yan sanda dangane da yadda su ka rika bai wa masu zanga-zanga kariya, kafin ta sauya salo zuwa tarzomar da ta hallaka ‘yan sanda masu yawa.

Ya ci gaba da cewa babu wani muzgunawa ko cin fuskar da zai hana jami’an ‘yan sanda gudanar da ayyukan su na tsaron lafiya, rayuka da dukiyoyin jama’a.

Share.

game da Author