Kwamitin zartaswar APC da ta yi zama yau Talata a Abuja, ta nuna alhini da rashin jin dadinta ga kisan da akeyi wa mutane a kasar nan na babu gaira babu dalili da kuma matsanancin rashin tsaro da ya addabi mutane.
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala ganawar Kwamitin ya ce jam’iyyar ba za ta lamunci a rika yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari cin fuska ba.
Idan ba a manta ba mambobin jam’iyyar PDP a majalisar tarayya sun yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari yayi murabus saboda acewar su gazawa da yayi wajen kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan.
Jam’iyyar APC ta gargadi ƴan adawa da su rika sara su na duban bakin gatari, kada cin fuskar ta yi yawa saboda santsin tsananin adawa ya kwashe su, su maida komai siyasa mana.
” Maimakon ƴan adawa su daɗa dagula abin kamata yayi su gane cewa maida matsalar tsaron kasar nan siyasa ba shine mafita ba.
A karshe gwamna El-Rufai ya bayyana wasu shawarwari da kwamitin zarataswar APC din ta dauka da suka hada da rusa duka kwamitin gudanarwar jam’iyyar tun daga Abuja har zuwa gundumomi.
Sannan da kara wa shugaban riko na jam’iyyar wasu watannin shida ya ci gaba da rike jam’iyyar.