Tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa, Seriake Dickson, ya yi nasarar zama Sanatan Bayelsa na Yamma a karkashin PDP, bayan da ya yi wa Peremobouwei na APC mummunan kaye da kuri’u masu tarin yawa.
A zaben cike gurabun da aka gudanar a ranar Asabar, 5 Ga Disamba, Dickson ya zama Sanata da kuri’u 115,257 a karkashin PDP, shi kuma Elebi na APC ya samu kuri’u 17,500 kacal.
Babban jami’in Zabe Farfesa Okechukwu Okeke na Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Otuake ne ya bayyana sakamakon zaben, tare da bayyana nasarar Dickson kan Elebi.
Dickson ya shafe shekaru takwas ya na mulkin Bayelsa. A zaben gwamna APC ta yi nasara a jihar, amma Kotun Koli ta soke zaben, saboda Mataimakin dan takarar Gwamna ya shiga zabe da takardun jabu.
Kotu ta soke zaben a ranar da ake shirin rantsar da dan takarar APC.
Bayan bayan saukar Dickson, an rantsar da dan takarar PDP a matsayin gwamna. Shi kuma Dickson ya fito takarar sanata a ranar Asabar da ta gabata, kuma ya yi nasara.
Wannan nasara ta nuna cewa PDP ce ta lashe zabukan sanata biyu na jihar Bayelsa, wadanda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta gudanar.
A daya zaben sanatan na Bayelsa, dan takarar PDP Abel Ebifomowei ne ya yi nasara a kan dan takarar APC.
Kafin zaben dai Karamin Ministan Fetur, Timeprey Sylva, wanda dan jihar Bayelsa ne, ya yi ta bugun kirjin cewa tun ma kafin rana ta take tsaka APC za ta lashe kujerun sanatocin biyu. Amma sai ga shi dan takarar APC ko kashi 13% bisa 100% na yawan kuri’un da Dickson ya samu, shi bai samu ba.
PREMIUM TIMES ta buga labarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna gamsuwa kan yadda aka gudanar da zabukan cike-gurabun a jihohi daban daban-daban.