Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 796 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum – 248, FCT-258, Kaduna-117, Katsina-52, Ogun-27, Kwara-23, Gombe-22, Adamawa-17, Filato-15, Kano-6, Rivers-2, Ondo-2, Ekiti-2, Nasarawa-2, Sokoto-2 da Taraba-1
Yanzu mutum 72,140 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 65,722 sun warke, 1,190 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 5,241 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 24,614, FCT –3,994, Oyo – 3,747, Edo –2,726, Delta –1,828, Rivers 3,116, Kano –1,880, Ogun–2,319, Kaduna –3,703, Katsina -1,171, Ondo –1,751, Borno –758, Gombe –1,069, Bauchi –802, Ebonyi –1,055, Filato – 3,994, Enugu –1,355, Abia – 926, Imo –681, Jigawa –340, Kwara –1,226, Bayelsa –466, Nasarawa – 541, Osun –965, Sokoto – 191, Niger – 298, Akwa Ibom – 362, Benue – 501, Adamawa – 304, Anambra – 290, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 108, Ekiti –391, Taraba- 196, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.
Gwamnatin Najeriya ta ce a gaggauta sake bude cibiyoyin killace masu cutar korona, ganin yadda cutar ta sake darkakar kasar gadan-gadan ba sauki.
Ministan Harkokin Lafiya Osagie Ehanire ne ya bayyana haka a wurin taron Kwamitin Dakile Cutar Korona a ranar Alhamis, a Abuja.
Ya ce yin hakan ya zama wajibi, ganin yadda korona ta sake darkakar kasashen Turai gadan-gadan, tamkar wutar-daji.
Ya ce a wannan karo kowa na da rawar da zai taka wajen ganin wannan cuta ba ta sake fantsama ta yi wa al’ummar kasar nan mummunan illa ba.
“Mun ga yadda a ‘yan kwanakin nan ake ta samun karuwar masu kamuwa da cutar korona a kullum a kasar nan. Wannan kuwa ya sa mu tunanin sake barkewar cutar a karo na biyu.
“Dalili kenan na bada umarnin a gaggauta sake bude cibiyoyin killace masu cutar korona da cibiyoyin bayar da magunguna wadanda a baya aka rufe, saboda karancin masu dauke da cutar. Kuma a sake gaggauta kai jami’an lafiya a dukkan cibiyoyin.
Kasahen Turai na ci gaba da samun adadin masu kamuwa da cutar a kullum, fiye ma da yadda aka rika samu a baya.
Kasashe irin su Ingila, Portugal da Hungary tuni sun rigaya har sun kakaba dokar zaman gida tilas, ganin yadda adadin masu kamuwa a kullum har ma ya zarce yawan irin yadda ta rika kama mutane a watannin baya.
Abin ya kara muni da kamari a Amurka, inda a yanzu adadin wadanda su ka kamu a kasar ya haura mutum milyan 15.
Minista Ehanire ya shawarci ‘yan Najeriya su dauki kwararan matakan kare kai, musamman a lokacin Kirsimeti da sabuwar shekara, domin cutar korona ba hutu ta ke dauka ko jin fashin ranar da ba a iya kamuwa da ita ba.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya sha alwashin cewa na Najeriya na sane da irin yadda cutar ta sake barkewar sosai a Turai, kuma ana cikin shiri a kasar nan.
Ya ce duk wasu rigakafi ko maganin korona da za a sayar wa Najeriya, zai kasance sai Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ingancin su tukunna.
“Kuma ko an kawo su a nan kasar, sai likitocin mu da masu binciken magunguna sun auna sun tantance sahihanci tukunna.” Inji Mustapha.