Dalilin da ya sa cikin wasu Ƴan siyasa ke durar ruwa da zaran an ambaci sake fasalin kasa – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana wasu dalilai da yake ganin sune ya sa wasu gaggan ƴan siyasan Najeriya basu son a sake fasalin kasar nan.

El-Rufai ya ce karara fargaban su shine muddun aka sake fasalin kasar nan, za su rasa madafa a siyasance, wato kamar tasu ta kare kenan.

Muhawara kan sake fasalin Najeriya ya dade ana ta kai komo akai na tsawon shekaru, sannan kuma ya haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin manyan ƴan siyasa da ƴan Najeriya.

Yayin da wasu ke nuna goyon baya ga ra’ayin bisa bukatar ingantaccen shugabanci, wasu ba su tare da wannan ra’ayi, a ganin su yin haka haka zai ruguza hadin kan kasar sannan kuma za su rasa madafa a siyasance.

Sai dai kuma El-Rufai a wata takarda ranar Talata ya ce ” sake fasalin kasa wani muhimmin abu ne da zai dace da tsarin shugabanci mai inganci a kasar nan.

” Yin hakan zai ba da damar ficewa daga tsarin wuce gona da iri da kuma sake daidaita tarayyar zama tare da gano iko da nauyin da ya rataya a matakan iko na gwamnati ta yadda kowani mataki na gwamnati zai iya wanzar da aiki yadda ya kamata.

Duk da dai bai ambaci sunan kowa ba, gwamna El-Rufai ya jaddada cewa akwai wadanda gaban su fadi yake da zaran an yi magana sake fasalin kasa saboda tsoron su shine shikenan tasu ta kare a siyasan ce. Wanda ba haka bane idan aka kwatanta da nasarorin da za a samu idan aka yi hakan.

” Muna so mu tabbatar musu cewa su kwantar da hankulansu, idan har hakan ya tabbata, zasu iya hada kai da mutane sannan su ma su cusa kan su cikin wannan canja da za a samu domin amafanin kan su da kasa baki daya.

Share.

game da Author