Dalibai sama da 300 suka bace a harin makarantar Kankara – Masari

0

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa an gano akalla mutum sama da 300 da suka bace ba san inda suka ba tun bayan harin da masu garkuwa suka kai makarantar sakandare na Kankara.

Masari ya ce akwai dalibai 884 a makarantar a lokacin da maharan suka afka makarantar. Yanzu babu dalibai 333.

Wannan shine jawabin da gwamna Masari yayi wa tawagar gwamnagtin tarayya da ta ziyarce shi a fadar gwamnati a Katsina.

Mai ba shugaban Kasa Muhammadu Buhari Shawara kan harkokin tsaron Kasa, Babagana Monguno ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa Katsina.

Shugaban Buhari na can jihar Katsina inda ya ke hutun mako guda a garin Daura.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikin sa ga harin da ƴan bindiga suka kai makarantar Sakandare dake Kankara, jihar Katsina ranar Juma’a.

Wannan hari ya zo a daidai shugaba Buhari na garin Daura inda ya tafi hutu.

Sannan kuma ya umarci jami’an tsaro su gaggauta ceto wadannan yaran makaranta sannan su kamo wadannan mahara.

Idan ba a manta ba a ranar Asabar gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari ya bada umarnin rufe dukkan makarantun kwanan Jihar Katsina, bayan ‘yan bindiga sun arce da daliban da ba a san adadin su ba.

Masari ya bada umarnin ne bayan da mahara da aka hakikance sun kai su 300 a kan babura suka kutsa sakandaren kwana ta garin Kankara, a Jihar Katsina.

Sun kutsa cikin makarantar wajen 11:30 na dare bayan sun harbe jami’in tsaro a kofar makarantar.

A cikin dare ranar Juma’a su ka kutsa cikin makarantar, bayan sun bindige jami’in tsaro na bakin kofar shiga. “Wannan lamari dai ya wuce tunanin mai tunani. Abin bakin ciki ne ainun ga al’ummar jihar Katsina. Amma ina tabbatar wa iyayen yara cewa duk wani yaron da ba a gani ba, za mu tabbatar da cewa mun ceto shi. Domin aikin mu shi ne kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

“A yanzu da na ke magana din nan, sojoji na can na bata-kashi da ‘yan bindiga. Ina rokon ku kara hakuri. Za a ceto dukkan daliban da aka yi garkuwa da su.” Inji Masari.

Masari ya kara tabbatar da cewa gwamnati za ta yi dukkan kokarin kawo karshen masu garkuwa da jama’a a jihar Katsina.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda aka sace yaran, sai dai kuma wasu bayanai sun nuna wasu yaran da dama sun bazama ne a cikin daji tsakar daren da abin ya faru.

Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tir da wannan hari, kuma ya umarci Babban Hafsan Sojoji Tukur Burutai ya tabbatar an ceto yaran ba tare da rasa ran yaro ko daya ba.

Share.

game da Author