Cocin Angilika ya dakatar da wani faston cocin da yayi lalata da matar wani faston

0

Cocin darikan Angilika na Najeriya ya dakatar da wani babban faston cocin dake jihar Ekiti, mai suna Rufus Adepoju bayan an kama shi da laifin saduwa da matar wani fasto cocin da yake jagoranta.

Bisa ga wasikar dakatar da faston daga aiki ranar 11 Disamba 2020 da PREMIUMTIMES ta gani ranar Talata ya nuna cewa Adepoju zai bar aiki na tsawon shekara daya sai dai babu tabbacin ko akwai horon da zai biyo bayan haka.

” Bayan gaisuwa cikin sunan Yesu Almasihu mai ceton mu, muna masu aika maka wannan wasikar dakatarwa daga shugabancin cocin Angalika saboda samun ka da laifin aikata fasikanci.

Bisa ga wasikar Adepoju zai mika shugabancin cocin zuwa ga mataimakinsa sannan ba zai sake taka cocin ba ko ya aikata wani aiki a matsayinsa na shugaban cocin ba har sai an dawo da shi.

Bayanai sun nuna cewa an nada Adepoju mai shekaru 57 shugaban cocin jihar Ekiti ranar 27 ga Yuni 2017.

Adepoju ya zama shugaban cocin ne bayan ya yi tsawon shekaru 37 yana aikin fasto da cocin Angilika.

Adepoju ya maya gurbin tsohon shugaban cocin Oludare Oke wanda ya yi ritaya a shekaru 70.

Tsohon shugaban cocin Oludare Oke ya ce za a iya samun cikakken bayanai game da Adepoju a wurin cocin Angilika ta Najeriya.

Share.

game da Author