CETO YARAN MAKARANTAN KANKARA: Buhari ya jinjina wa Masari

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yanzu haka yake garin Daura yana hutu, ya jinjina wa gwamnan Katsina Aminu Bello Masari bisa kokarin da yayi wajen ceto yaran makarantan Sakandaren Kankara da aka sace.

A ranar Alhamis ne ‘yan bindiga suka sako yaran makaranta sama da 300 da aka sace a Kanakara.

Bayan nan kuma ya yabawa jami’an tsaron da aka fafata dasu wajen tattauna ceto yaran.

A karshe ya roki ‘yan Najeriya su ci gaba da hakuri da gwamnati a wannan lokaci da take fama da matsalolin tsaro, tattalin arziki da rayuwan mutan kasa.

Yadda muke ceto yaran makaranta

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana yadda gwamnati da makarrabanta suka ceto yaran makarantan Kankara da masu garkuwa da mutane suka arce da su.

A wata hira da yayi da DW ta Jamus, Masari ya ce an hada da jami’an tsaro da wasu jami’an gwamnati wajen tattaunawa da masu garkuwan har aka iya ceto su.

” Sannan kuma ko sisi gwamnati bata ba su ba, tattaunawa ta yi da su har aka cimma matsaya suka saki yaran.

Masari ya kara da cewa ba Boko Haram bane suka sace yaran, yan bindiga ne tsangwararan suka tafi da yaran cikin daji.

Ya kuma kara da cewa za a kai taho da yaran garin Katsina domin likitoci su duba su sannan kuma sannan a basu kayan sawa su canja na jikin su. Daga nan sai a mika su ga iyayen su.

Akalla yaran makaranta sama da 300 ne ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su.

Wani mutum mai suna Aminu Male, ya bayyana yadda wasu makiyaya su ka cinto dan sa a jeji, bayan ya kubuta daga hannun wadanda su ka saci daliban sakandare su 333 a Kankara, Jihar Katsina.

Male ya ce makiyayan ne su ka tsinto dan sa, kuma su ka kai shi masa dan gida.

Tuni dai Boko Haram su ka yi ikirarin sace yaran, kamar yadda wani faifai ya bayyana Shekau na bayani.

Yaron mai suna Usama, ya na da shekaru 17, sannan ya na babban aji na SS2 a Sakandaren Kimiyya ta Kankara.

Bayan an kai masu hari an tafi da su a ranar Juma’a tsakar dare, ya taki sa’ar kubuta, aka maida shi gida ranar Lahadi.

Dalibin ya shaida wa baban sa cewa an rika yi doguwar tafiya da su a cikin surkukin jeji mai nisan gaske.

Ya ce sai cikin dare ne kawai ake tarkata su a tasa su gaba ana kara nausawa cikin jeji da su. Ya ce amma da rana ana boye su cikin bishiyoyi masu duhu, don kada jiragen helikwafta masu shawagi su gano su.

Share.

game da Author