Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa ‘yan uwa da iyalan marigayi Sam Nda-Isaiah wanda ya rasu ranar Juma’a da dare.
Sam Nda-Isaiah, wanda mawallafin jaridar Leadership ne ya rasu bayan wata ‘yar gajeruwar rashin lafiya da yayi.
Buhari ya bayyana Sam a matsayin abokin aiki kuma mutumin kirki sannan ya roki Allah ya ba iyalansa jure wannan rashi.