Buhari fa ba ‘marowacin shugaba’ ba ne, akwai kyauta – Inji Femi Adesina

0

Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari na Musamman a Bangaren Yada Labarai, Femi Adesina, ya bayyana yadda Buhari ya sha taimaka masa da kudi ya na fita-kunya, a duk lokacin da fatara ta sa ya kasa kawar wa kan sa matsalolin yau da kullum.

Adesina ya ce duk da Buhari na ikirarin cewa shi marowaci ne, to har daloli ya taba dauka y aba shi a lokacin da Femi din zai yi wata tafiya zuwa China, domin halartar wani kwas na kwanaki 12 a can.

An dai shirya kwas din ga manyan jami’an gwamnati.

Adesina ya yi wadannan bayanan cikin wani rubutu da ya yi domin taya Buhari murnar ya cika shekaru 78 a duniya. Ya fito da rubutun a yau Alhamis, 17 Ga Disamba, ranar zagayowar ranar haihuwar Buhari.

“Cikin Janairu 2017, an ba ni sarautar gargajiya ta Nwanne di Namba na Daular Mmaku da ke cikin Jihar Enugu. To da zan je nadi na shaida wa Shugaba Buhari. Haka wannan bawan Allah da ke kiran kan sa marowaci, ya dauko masu kauri y aba ni domin na dauki nauyin abokai na su raka ni. Ba zan shaida maku adadin da ya ba ni ba. Don kada ku roke ni neman ragowar sauran canjin.”

“Cikin watan Mayu, 2018 da tafiya ta kama ni zuwa China, ana saura kwana biyu na je na sanar da shi. Ya ce min Adesina na san ba ka da kudi, amma ka na jin kunyar ka roke ni. Haka ya dauko anbulan cike da kudin kasashen waje ya damka min. Eho, kwalelen ku. Ba zan fada maku ko nawa aka ba ni ba,”

Rubutun na Adesina dai ya na kokarin nuna cewa ogan na sa karimi ne, duk kuwa da sukar sa da ake yawan yi cewa dunkulallen hannu gare shi, ba ya kyauta.

Ya ce da jama’a da dama za su samu damar kusantar sa, za su gane cewa mutum ne mai dadin zama da saukin sha’ani.

Ya ce ya san mutane za su ce ai dole ya yabi Buhari, tunda a karkashin sa ya ke. Ya ce amma ba haka ba ne. Da ya ga dama, sai ya yi wa Shugaba Buhari aiki ba tare da an biya shi albashin ko sisi ba.

Adesina ya kara tunatar da jama’a cewa nan da shekaru biyu da watanni Buhari zai sauka daga mulki da yardar Allah. Zai koma Daura ya yi zaman sa a lokacin da ya cika shekaru 80 a duniya.

A karshe ya ce idan aka ci gaba da kokarin hargitsa masa shirye-shirye, to ‘yan Najeriya ne za su yi asara. Wata rana za a ce ina ma Buhari ne a kan mulki. Za a yi kewar sa a kasar nan.

Adesina ya rika bayyana irin zumuncin Buhari, yadda ya ke kiran Kiristoci ya na taya su murnar Kirsimeti.

Share.

game da Author