Shugaba Muhammadu Buhari ba zai bada kai ga bori, kurari da matsin-lambar wasu marasa kishin kasa ba, wadanda ba su iya komai ba sai suka, babu abin yabon da su ke gani ga gwamnati. Fadar Shugaban Kasa ce ta maida wannan kakkausan martani.
Kakakin Yada Labarai na Buhari ne, Garba Shehu ya nanata haka a ranar Juma’a a shafin sa na Tweeter.
Musamman Garba na magana ne kan wadanda ke yanko magana babu aunawa a sikeli ko mizanin rashin dacewar ta, su na cewa, “Najeriya za ta dare gida-gida”.
A kan wannan ne kakakin na Buhari ya ce Buhari ba zai taba daukar wani matakin da ‘yan Najeriya za su cutu ba.
“Fadar Shugaban Kasa na magana ne a kan wasu ‘yan giribtu wadanda babu wani alheri a zukatan su, sai furta munanan kalamai na barazanar kiran Shugaban Kasa ya yi wani abin da su ke so, a lokacin da su ke so, ko kuma a na su shirmen, idan ba a yi abin da su ke so din ba, to kasar ta rabu bangare-bangare.”
“To wannan kakkausan gargadi ne ga wadannan marasa kishin kasa cewa Shugaba Buhari ba zai bada kai bori, kurari ko wata barazanar su ta sa ya sauka daga turbar da ya ke a kai ta inganta kasar nan ba. Musamman a wannan lokaci da ake fuskantar gagarimin kalubale na tsaro a yanayin da annobar korona ta taso kasar nan da ma duniya a gaba.
“Shugaba Buhari shugaba ne da aka zaba kuma zai ci gaba da yin aiki tare da masu kishi a kasar nan, domin ganin ya samar da mafita daga matsaloli da kalubalen da kasa ke ciki, wadanda su ka zame wa Najeriya tarnaki da alakakai wajen samun cigaba a kasar nan.”
Shehu ya ce Buhari ba shi ma da lokacin saurare ko maida hankali ga ‘yan soki-burutsu, domin ayyukan magance tsaro da cutar korona su ya tasa a gaba, a halin yanzu.