BOKO HARAM: Idan ba a tashi tsaye ba, ƴan ta’adda za su lakume Najeriya – Gwamnonin Najeriya

0

Gwamnonin Najeriya sun bayyana cewa idan fa ba a tashi tsaye an yi da gaske ba, to ‘yan ta’adda da kuma sauran ‘yan bindiga za su iya tarwatsa Arewa, su lakume ta baki daya.

Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya ne ya fadi haka, a Maiduguri, lokacin da ya je ta’aziyya, jaje da taya alhini ga Gwamna Babagana Zulum na Barno.

Fayemi ya je taya alhini kisan yankan rago ne da Boko Haram su ka yi wa manoma 43 a kauyen Zabarmari cikin Karamar Hukumar Jere, a Jihar Barno.

Majiya a Zabarmari ta shaida wa PRWMIU TIMES cewa an yi wa manoman yankan rago ne a lokacin da su ke aikin shinkafa a Garin Kwashebe.

An kai masu harin ne a lokacin da al’ummar Jihar Barno su ka raja’a wajen zaben Kananan Hukumomin jihar a ranar Asabar.

Duk da an binne wadanda aka kashe din su 43, mazauna yankin sun ce akwai wasu masu aiki a gonar shinkafar wadanda har yau babu labarin su.

A cikin wani bidiyo na minti uku, bangaren Shekau na Boko Haram ya yi ikirarin kisan manoman, wadanda ya ce su 78 ne su ka yi wa yankan rago, ba 43 ba.

Fayemi a wurin ta’aziyya ya bayyana kisan da cewa dabbanci ne, wanda ya zama wajibi tashi tsaye domin a dakile Boko Haram da sauran maharan da su ka hana Arewa zama lafiya, ko kuma su tarwatsa kasar ta hanyar lakume Arewa baki dayan ta.

Fayemi ya tunatar da irin kokarin da gwamnonin kasar nan su ka yi wajen zaman ganawa da Shugaban Kasa da kuma Shugabannin Tsaron Najeriya a kan matsalolin ta’addanci, amma had yau babu wata alamar nasara.

Daga karshe ya ce a gaskiya ayyukan tsaron kasa ya sha kan sojojin Najeriya, ganin yadda su ka shafe shekaru goma cur su na yaki da ta’addanci.

Share.

game da Author