BINCIKEN KWAKWAF: Yadda Ma’aikatar Lafiya ta yi wa ma’aikatan ta watandar naira bilyan 2.4 na kudaden jinyar marasa lafiya

0

Kimanin naira bilyan 2 da milyan 400 ne Ma’aikatar Lafiya ta Kasa ta yi wa ma’aikatan ta watanda da su, a cikin watanni ukun karshen shekarar 2019.

Binciken da PREMIUM TIMES ta yi a rumbun tattara bayanan intanet na Ma’aikatar Lafiya ne ya tabbatar da haka.

A baya PREMIUM TIMES ta fallasa ire-iren wadannan harkalla da zambar makudan kudade a ma’aikatun gwamnatin tarayya da dama, ciki har da Ma’aikatar Lantarki lokacin ta na karkashin Minista Babatunde Fashola da kuma Hukumar Bunkasa Garuruwan Kan Iyakokin Najeriya, wanda shugaban ta, suruki ne ga Shugaba Muhammadu Buhari.

Dalla-dalla: Watandar Naira Bilyan 2.4 Ta Kula Da Marasa Lafiya:

1. Ma’aikata 25 ne kacal aka yi wa watandar kudaden.

2. An rika tsinka masu kudaden a hankali cikin watanni hudu, wato daga Satumba, Oktoba, Nuwamba zuwa Disamba.

3. Jimla da adadin kudaden sun kai naira 2,400,759,805.90.

4. PREMIUM TIMES ta rubuta wa Ma’aikatar Lafiya ta Kasa wasikar neman a ba ta iznin duba wasu bayanai an hana ta. Kuma ma’aikatar ta kasa bayanin dalilin yin watandar kudaden, duk da cewa yin hakan, take dokar kasa ce kuru-kuru.

5. Mutum 5 daga cikin 25 din aka tura wa kashi 86% bisa 100% na adadin kudaden, wato naira bilyan biyu

6. Manyan ‘Yanlele 5 Da Aka Yi Wa Watandar Naira Bilyan 2:

Bulam Sadiq Isa: An zabga masa naira milyan 671 cikin asusu. An tsitstsinka masa kudaden sau 83, don bagaraswa.

Musa Adamu: An gabza masa naira milyan 471.5. Sau 28 aka antaya masa kudaden domin bad-da-bami.

Ajiji Barde Yusuf: An dumbuza masa naira milyan 394. Shi kuma sau 63 aka tsinka masa kudaden a cikin watanni hudu.

Adama Mohammed Danladi: Naira milyan 395 aka rika tsinka masa sau 110, duk aka antaya a asusun sa, don bugar da mai bin kwakwaf.

Mohammed Badegi Mohammed: An tsinka masa naira milyan 175 sau 30, don kada ‘yantsurku su gane.

7. An raba sauran naira milyan 400 ga ma’aikata su 20.

8. Doka ta Babi na 7, Sashe na 701 da na 713 duk sun ce babban laifi ne a tura kudaden gwamnati a aljihu ko asusun ajiyar banki na ma’aikacin gwamnati.

PREMIUM TIMES ta rubuta takardar neman karin bayani ta aika a ranar 28 Ga Oktoba. Babu amsa, sai a cikin Nowamba aka amsa cewa ana kokarin duba zarge-zargen kudaden da jaridar nan ta ce an yi watanda da su.

Jadawalin Ma’aikata 25 Da Aka Yi Wa Watandar Naira Bilyan 2.4:

1 – BULAM, MR. SADIQ ABUBAKAR – 671,996,049.00

2 – MUSA ADAMU MUSA – 471,493,235.00

3 – AJIJI, MR. BARDE YUSUF – 392,350,175.16

4 – ADAMA MOHAMMED DANLADI – 355,911,809.80

5 – MOHAMMED BADEGGI MOHAMMED – 175,015,182.00

6 – IBRAHIM, MR. Y MOHAMMED – 57,004,800.00

7 – DOROTHY NKIRUKA EZEOKPUBE – 40,652,000.00

8 – ALI UMAR – 39,339,000.00

9 – ADEGBITE, MRS. BOLA OLUWAFUNMILOLA – 34,904,912.00

10 – OSIBE, MR. EMMANUEL EJIKE – 18,881,200.00

11 – KESHIRO, MR. IBUKUN BONIFACE – 15,753,271.94

12 – SANNI ADENIYI, MRS. ADETORO OLUFUNMILAYO – 14,949,240.00

13 – AKWUH, MR. ISRAEL SHAIBU – 11,803,200.00

14 – ULOKO, MR. DANIEL SUNDAY – 11,448,000.00

15 – ALONGE, DR. OLUWATOYIN BOLADALE – 11,388,200.00

16 – GODWIN BROOKS ASUQUO – 10,836,800.00

17 – SHENKOYA, ESTHER ABIODUN – 10,399,429.00

18 – TOYE, MR. ADEDOKUN FEMI – 9,398,000.00

19 – ADAMU PAIKO MAMUD – 8,820,622.00

20 – OLOWU, DR. ROSEMARY OMOBOLANLE – 7,571,950.00

21 – SEMLEK, MRS. NAWOK RACHEL – 6,874,130.00

22 – IKE, MR. MADUABUCHI SUNDAY – 6,553,000.00

23 – ANYANWU, MR. CHINEDU LAWRENCE – 6,132,000.00

24 – ONOJA, MR. OCHE GEORGE – 5,907,600.00

25 – IDRIS, MR. ABDULLAHI – 5,376,000.00

= 2,400,759,805.9

Share.

game da Author