Sakataren kwamitin mazabar Duguri (WDC) dake karamar hukumar Alkaleri jihar Bauchi Adamu Suleiman ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta kawo wa kauyen Duguri dauki saboda macizai sun addabe su a kauyen.
Suleiman ya fadi haka ne ranar Laraba da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Duguri.
Ya ce daga watan Mayu zuwa Nuwanban 2020 macizai sun sari mutum 47 a kauyen.
“Daga watan Mayu zuwa Nuwanba mutum biyar sun mutu a dalilin saran maciji sannan mutum 37 na kwance a asibitocin dake jihohin Filato da Gombe.
Suleiman ya ce macizai sun addabe su a kauyen ne saboda kusantar kauyen da wurin shakatawa na Yankari dake jihar.
Ya ce an yi feshi Kuma an saka magani amma abu ta ki ci ta ki cinyewa.
Suleiman ya ce a yanzu haka manoma sun buge da saka takalman roba, safan hannu da tabarau domin samun kariya daga cizon macizai yayin da suke aiki a gona.
Sannan likitoci da masu maganin gargajiya sun hada hannu domin ganin sun warkar da mutanen da macizai ya sara.
Suleiman ya yi kira ga gwamnati da ta rage farashin maganin sarar maciji saboda talakawa su iya siyan maganin.
Rabi Duguri mai shekara 20 da maciji ya sareta ta yi kira ga gwamnati da ta taimaka mata da kudin magani.
Rabi ta ce zuwa yanzu ta kashe Naira 200,000 amma har yanzu sauki bai samu ba.
A ranar 2 ga Oktoba PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda cibiyar gudanar da bincike kan dafin maciji dake jami’ar Bayero a Kano (BUK) ta horas da ma’aikatan kiwon lafiya 50 kan hanyoyin kula da mutanen da maciji ya sara.
Discussion about this post