BARNO: Sojoji sun kashe Boko Haram 9, sun kwato makaman su

0

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta bayyana cewa Zaratan Sojan ‘Operation Fire Ball, sun kashe Boko Haram da ‘yan ta’addar ISWAP a wasu hare-hare biyu mabambanta da sojojin su ka kai a Barno.

Daraktan Yada Labarai na Riko, Barnerd Onyeuko ne ya tabbatar da haka, inda har ya kara da cewa an samu nasarar cin ganimar motar su ta yaki da kuma tulin makamai masu tarin yawa.

Onyeuko ya ce tun da farko sojoji sun kashe Boko Haram hudu wadanda su ka yi gangancin kokarin kai wa Sansanin Soja na 17 da ke Cross-Kauwa hari.

Ya ce amma nan da nan sojojin runduna ta 401 ta Zaratan Musamman ta maida masu martani, ta kashe mahara hudu kuma ta ji wa da dama daga cikin su raunuka.

A wannan nasarar ce aka kama motocin yakin su biyu sa sauran makamai masu yawa, cikin har da manyan bindigogin harbo helikwafta.

Ya kara da cewa sojojin runduna ta 11 da ke Kenuba sun kashe Boko Haram 5, kuma su ka ji wa da dama rauni.

Onyeuko ya tabbatar wa jama’a cewa sojojin Najeriya za su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da kare lafiya da dukiyoyin jama’a.

Ya yi rokon cewa mutane su rika bada rahotannin duk inda su ka ga ko su ka ji kishin-kishin din bullar batagari da sauran ‘yan ta’adda.

Har yau dai ana jmamin kisan mutum 43 da Boko Haram su ka yi wa yankan rago, wadanda dukkan su manoma ne a Zabarmari, cikin Karamar Hukumar Jere ta Jihar Barno.

Share.

game da Author