Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kaduna ta sanar da rufe makarantun jihar Kaf daga ranar Talata saboda barkewar annobar Korona da ya darkako jihar baba kakkautawa.
Kwamishinan Ilmin Jihar, Shehu Muhammad ya sanar da haka a wata takarda da ma’aikatar ta fitar ranar Litinin.
Gwamnati ta umaci kowacce makaranta ta kammala jarabawa ranar Talata sannan ta rufe makarantar ranar Laraba.
” Yin haka ya zama dole ganin yadda Korona ta darkako jihar babu kakkautawa a karo na biyu.”
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da ake samun yawa-yawan mutanen da suka kamu da cutar a wannan karo na biyu.
A kusan kullum sai an samu karin mutum sama da 100 da suka kamu da cutar a fadin jihar.
Kwamishina Shehu ya ce Iyaye su samar wa ‘ya’yan su yadda za su cigaba da karatu a gida yanzu. Sannan kuma makarantun da ke iya karantar da yara ta yanar gizo sai su ci gaba.
Haka kuma suma manyan makarantun jihar, an umarce su da su tsara yadda dalibansu za su ci gaba da karatu daga ranar Laraba.
A karshe gwamnati ta umarci iyaye su kula da ‘ya’yan su sanna a ci gaba da bin dokokin Korona kamar yadda ma’aikatar kiwon Lafiya ta sanar.
Discussion about this post