Gwamnatin jihar Adamawa ta bayyana cewa za ta ci gaba da yi wa yara allurar rigakafin cutar bakon dauro a jihar.
Gwamnatin ta kuma ce za ta yi wa yara ‘yan ƙasa da shekara biyar su akalla 280,000 allurar rigakafin cutar domin dakile yaduwar ta a jihar.
Gwamnan jihar Ahmadu Fintiri ya sanar da haka a a wajen kaddamar da fara yi wa yara rigakafin da ake yi a cibiyar kiwon lafiya na matakin farko dake Luggere a Yola ranar Litini.
Fintiri ya ce gwamnati ta zara matsa kaimi wajen ganin an yiwa kowani yaro rigakafin cutar, domin rage yawan mace-mace da ake fama da shi.
Cutar na yaduwa ne idan mai dauke da ita ya yi tarin ko atishawa kuma kana kusa da shi.
Alamun cutar sun hada da atishawa, zazzabi, yawan kukan yaro, ciwon jiki, rashin iya cin abinci da dai sauran su.
Cutar na ajalin yara Idan ba a gaggauta neman magani ba ko zuwa asibiti da wuri ba.
Fintiri ya ce bincike ya nuna cewa Najeriya na daya daga cikin kasashen da wannan cuta ta yi tsanani a cikinta cikin kasashen duniyan da ke fama da cutar.
A karshe, gwamnan ya yi kira ga duk iyaye da su tabbatar ‘ya’yan su sun yi allurar rigakafin cutar da aka Fara a jihar.